Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da kisan Sojoji da yan sa kai 60, Buhari ya tura tawagar jaje
- Shugaba Muhammadu Buhari ya tura Ministan harkokin waje taya shi ta'azziya da al'ummar jihar Kebbi
- Gwamnatin Kebbi tace a baya basu fuskantar matsalar yan bindiga amma yanzu abin ya dawo kansu
- Mazauna garin da majiya daga jami'an tsaro sun ce an kashe sojoji 13, yan sanda guda biyar da wani dan sakai daya sannan wasu sun jikkata
Birnin Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da kisan hafsoshin hukumar Sojoji da tsagerun yan bindiga daga jihar Neja suka yi a Kebbi.
Rahotanni sun bayyana yadda yan bindiga suka hallaka Sojoji da 'Yan Sa Kai' a kauyen Majuju dake karamar hukumar Sakaba ta jihar.
Gwamnan jihar, Atiku Bagudu, yayin karban bakuncin tawagar Shugaba Buhari ya tabbatar da wannan hari., rahoton tvcnewsng
Bagudu ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar Babale Umar Yauri.
Shugaba Buhari ya tura wakilan gwamnatin tarayya jajantawa Gwamnatin Kebi karkashin jagorancin Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.
Mai magana da yawun Gwamnan Kei, Yahaya Sarki, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa Gwamna Atiku yace a baya babu yan bindiga a jiharsa amma yanzu sun fara shigowa.
Shugaban tawagar jaje da Buhari yace:
"Shi yasa Shugaban kasa ya turo mu don mika sakon ta'azziyar da kasashen waje suka yi. Ya kamata mu cigaba da zage dantse saboda zamuyi nasara."
Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da yan sa kai 60
Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 19 cikinsu akwai sojoji 13, a jihar Kebbi, a cewar wata majiyar tsaro da mazauna gari a ranar Laraba.
An yi artabun ne a daren ranar Talata a kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, kwana guda bayan an kashe dimbin yan sakai a yankin.
Daruruwan yan bindiga sun afka Kanya, inda suka fafata da sojoji da yan sanda na tsawon awa uku a cewar majiya da kuma mazauna garin.
Wani mazaunin garin da ya ce sunansa Musa Arzika, wanda shima ya tabbatar da adadin ya ce maharan sun taho ne a kan babura 200, kowanne mutum uku a kai, suka afka wa kauyen.
Asali: Legit.ng