2023: Tsayar Da Jonathan Takara Zai Kwantar Da Tarzomar Kudu Maso Gabas, Ƙungiya

2023: Tsayar Da Jonathan Takara Zai Kwantar Da Tarzomar Kudu Maso Gabas, Ƙungiya

  • Wata kungiyar siyasa mai suna Southern Network for Good Governance ta ce idan Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2023 zai kwantar da kurar kudu maso gabas
  • An dinga cece-kuce akan batun ya kamata jam’iyyu su tsayar da ‘yan takarar shugaban kasar su daga kudancin kasar nan, duk da dai tsohon shugaban kasar bai nuna burinsa na tsayawa takara ba
  • A ranar Talata, Emmanuel Chukwuemeka, mai gudanar da kungiyar ya ce idan aka tsayar da Jonathan takara, ko wanne yankin kasar nan zai daidaita

Wata kungiyar siyasa mai suna Southern Network for Good Governance ta yi magana dangane da tsayawa takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a zaben 2023 da ke karatowa, The Cable ta ruwaito.

An dinga matsa lamba akan dacewar jam’iyyu su tsayar da ‘yan takarar shugaban kasar su daga yankin kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

2023: Tsayar Da Jonathan Takara Zai Kwantar Da Tarzomar Kudu Maso Gabas, Ƙungiya
2023: Tsayar Da Jonathan Takara Zai Kwantar Da Hankulan Yan Kudu Maso Gabas, Ƙungiya. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Tsohon shugaban kasar bai riga ya nuna burinsa na tsayawa takarar ba har yanzu.

Jonathan zai daidaita ko wanne yankuna

A wata takarda wacce Emmanuel Chukwuemeka, shugaban gudanar da kungiyar ya saki, ya ce idan aka tsayar da Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa, zai kawo daidaito ga ko wanne yanki.

A cewar Chukwuemeka:

“Takarar GEJ za ta kawo zaman lafiya da kwanciyar hankalin ko wanne yankin da ke kasar nan.
“Yankin kudu maso yamma suna ta kunno wuta akan a tsayar da wani daga yankin su, kuma GEJ ya samar da nasarori wurin gyara a kasar nan.
“Tsayar da GEJ takara zai kawo kwanciyar tarzoma musamman ga matasan yankin kudu maso gabas wadanda suka dinga daga hankali akan a daidaita yankin su da sauran yankuna.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Jonathan adali ne, a cewar kungiyar

Shugaban kungiyar ya ce babu wanda zai ji tsoro don an tsayar da Jonathan kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Ya riga ya nuna cewa mutum ne shi mai nuna wa kowa so da kauna tare da zubar da batun kungiyanci, addini da kuma siyasa yayin gudanar da mulki.
“Jonathan mutum ne wanda aka riga aka auna shi kuma aka gane cewa mutum ne wanda ya kware a harkar mulki da adalci. Muna bukatar mutum irin shi don ya jagoranci kasa.”

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164