Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina

Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina

Katsina - Masu garkuwa da mutane sun sako dagaci da sauran mutane 35, bayan biyan N26 miliyan a matsayin kudin fansa, bayan wadanda aka yi garkuwan dasu sun kwashe kwana 29 a hannun 'yan bindigan kafin su sake su a yammacin Lahadi.

'Yan bindiga sun sako dagacin Guga cikin karamar hukumar Bakorin jihar Katsina, Alhaji Umar da sauran mazauna kauyen guda 35 bayan amsar N26 miliyan a matsayin kudin fansa.

Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina
Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Premium Times ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga kauyen a ranar 7 ga watan Fabrairu, inda suka halaka mazauna yankin guda 10 daga bisani suka yi awon gaba da mutane 36, duk da dagacin kauyen.

Babban da da sirikin basaraken ne suka tabbatar da sakin wadanda aka yi garkuwan dasu a daren Litinin.

Kudin fansa

Kamar yadda sirikin, Nafiu Muhammadu ya ce, 'yan bindigan sun tuntubi iyalin bayan kwana biyu da garkuwa dasu, inda suka bukaci N30 miliyan a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

An Kuma: Yan bindiga sun sake kai mummunan harin jihar Arewa, sun bindige dandazon mutane

"Sun yi ta ciniki da kanin dagacin da wasu daga cikin dattawan anguwan. Sai dai a lokacin da aka sanar dasu cewa ba za a iya biyan su kudin da suka bukata ba, sun yi alkawarin tattaunawa da shugabansu sannan su sake tuntubar su, inda suka yi hakan bayan kwana uku," a cewarsa.

Muhammadu ya ce, yayin da 'yan bindigan suka sake kira, sun bukaci N10 miliyan, tare da jan kunne da kada a sake neman ragi.

"Sun ce sun san shi (dagacin) yana da kudi saboda haka, mu nemo N5 miliyan don amsar shi da kuma N5 miliyan na sauran mazaunan kauyen," Muhammadu ya kara.

Amma a lokacin da me kai kudin fansar ya kai wa 'yan bindigan N10 miliyan, sun shaida masa cewa za su amsa wannan kudin a matsayin diyyar wasu 'yan bindiga da 'yan sa kai suka halaka a yankin.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun sace mata da miji, sun hada da jariri mai wata 5

"Mun razana," a cewar Abdullahi Umar, dan dagacin. "Sun ce muje mu karo N20 miliyan idan da gaske muna son ceton mutanen mu. Haka nan muka koma muka tattara N16 miliyan, inda daga bisani suka umarce mu da mu koma gida mu jira dawowar mutanen mu."

Umar ya ce, wadanda aka yi garkuwan dasu sun dawo Guga da yamma, inda ma'aikatan lafiya suka duba su, Premium Times ta ruwaito.

A lokacin da aka tambaye su yadda suka samu N26 miliyan din, Umar ya ce, sun saida duk abubuwan da suka mallaka sannan suka nemi taimakon wasu attajirai a cikin jihar.

Ya kara da bayyana yadda aka bukaci duk dan garin, har da wadanda ba a yi garkuwa da 'yan uwan su ba da su bada nasu gudunmawa.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun halaka rayuka 2, sun sace mutum 1, tare da jigata wasu 3

A wani labari na daban, tashin hankali ya dawo ga anguwar Nasarawa-Burkullu, yayin da 'yan ta'adda suka kai wa rundunar 'yan sandan farmaki.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

Hatsabiban sun yi garkuwa da mutum daya, tare da halaka mutane biyu, sannan suka raunata mutane uku yayin kai harin misalin karfe 6:50 na yamma, a ranar 2 ga watan Maris, 2022.

Anguwan Nasarawa-Burkullu na cikin karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, a arewa maso yammacin Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng