An damke dan sandan bogi yana amfani da kayan sarki wajen damfarar mutane
- An damke wani matashi mai amfani da kayan yan sanda wajen damfarar yan kasuwa a jihar Kano
- Yan kasuwan sun bayyana cewa yana zuwa ya saya kaya da Taransfan karya sannan ya jiye lambar wayarsa
- Matashin ya amsa laifin da yayi kuma ya yi nadamar abubuwan da yayi
Bampai, jihar Kano - Jami'an hukumar yan sanda a jihar Kano sun damke wani dan sandan bogi wanda ake zargi da damfarar yan kasuwa ta hanyar Transfa na karya.
Matashin mai suna Yusuf Abdullahi, ya shiga hannu ne bayan wasu daga cikin yan kasuwan da ya damfara suka kai kararsa ofishin hukumar yan sanda.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana wannan matashi a bidiyo tare da yi masa tambayoyi
Kiyawa yace:
"Wannan mutum akwai korafe-korafe da muka samu daga wajen mutane uku cewa wani ya je da kayan yan sanda ya gabatar da kansa kuma yayi sayayya hannunsu, ya tura kudi basu ga alert be amma ganin yana sanye da kayan yan sanda suka bashi suka karbi lambar wayansa"
"Tun daga nan idan suka kirashi a waya yaki dauka"
Hira da wadanda ya damfara
Kiyawa yayi hira da wadanda suka shigar da shi kara don bayyana yadda yayi sayayya wajensu kuma yayi musu Taransfan karya.
Kowanne cikin yan kasuwan sun bayyana kudin kayan da ya damfaresu da kuma yadda suka yi.
Ya sayi kayan N6000 hannun dan kasuwan farko, N25,000 hannun mai takalma, kuma kayan N55,000 hannun mai gas.
Kalli bidiyon:
Kiyawa ya yi kira ga mutane su daina saurin yarda da mutum don ya sanya kayan yan sanda.
An damke irinsa a jihar Ondo
Jami'an hukumar yan sandan jihar Ondo sun damke wani mutumi mai suna Nkanu Patrick wanda ke ikirarin shi mataimakin Sufritanda ASP ne.
TVCNews ta ruwaito cewa jami'an yan sandan yankin Ore dake yawon sintiri suka damke mutumin a babban Benin/Ore Expressway.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce an damkeshi ne yana raka wata mota kirar Volkswagen dauke da magunguna inda suka nufi birnin Benin.
Asali: Legit.ng