Da duminsa: 'Yan ta'adda sun bindige mai gadi, sun yi awon gaba da faston cocin katolika
- Wasu miyagun 'yan ta'adda sun kutsa yankin Kudenda da ke jihar Kaduna inda suka halaka mai gadi tare da sace fasto
- An gano cewa sun kutsa yankin wurin karfe 1 na daren Talata inda suka dinga harbe-harbe inda daga bisani suka dauke Rabaren Joseph Akeke
- Mazauna yankin sun ce an hada da wata mata tare da yaranta biyu yayin da aka tasa keyar faston, kuma ba su iya bacci ba saboda firgici
Kaduna - 'Yan bindiga sun halaka rayuka biyu tare da sace babban faston cocin katolika, Rabaren Joseph Akeke, a yankin Kudendan da ke jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne wurin karfe 1 na dare Talata yayin da 'yan bindiga suka kutsa yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Wani mazaunin yankin mai suna Samson ya sanar da Daily Trust cewa miyagun sun kammala barnar wurin karfe biyu da rabi na dare.
Ya ce wadanda aka kashe duk masu gadi ne a gidan Rabaren din, yayin da wani makwabcin faston yace sun hada da wata mata tare da yaranta biyu sun sace
"Mun kasa bacci a daren jiya saboda tashin hankalin da muka fada sakamakon harbe-harben da muka dinga ji. Rabaren din shi ne babban faston cocin katolika ta Kudenda. An kashe mai gadinsa. An kashe wani mutum kuma sun hada da wata mata tare da yaranta biyu sun sace," yace.
Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Jalige Mohammed, ya cez ai nemo karin bayani kan lamarin kafin yayi tsokaci.
ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS
A wani labari na daban, bayan wani binciken sirri da hukumar tsaron farin kaya tayi, ta ce ta gano yadda mayakan ISWAP ke horar da masu kunar bakin wake yadda za su kai hari ga jami'an tsaro da yankunan kasar nan.
Haka zalika, DSS ta bayyana yadda wasu daga cikin ISGS dake yankin tafkin Cadi, wadanda suka yi hijira zuwa Mali, bayan takura musu da sojojin da rasha tayi haya suka yi, inda suka shigo kasar Najeriya don karfafa ayyukan yan ta'addan ISWAP, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban SDES na jihohin arewa maso gabas, Babagana Bulama, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Hukumar ta hada taron, domin ta duba kalubalen dake tunkaro yankin, TheCable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng