Insha Allah zamu maida Magidanta 500 gidajen su, mu basu N100,000 su ja jari kafin Ramadan, Zulum
- Gwamna Zulum na Borno ya ce gwamnatinsa zata yi kokarin maida magidanta 500 daga Malam-Fatori gidajen su kafin watan Ramadan
- Zulum ya ce Insha Allahu gwanatinsa zata maida su gida tare da tallafin N100,000 ga kowane mutum ɗaya
- A cewarsa wannan shi ne lokacin da ya dace, Magidanta ruwa ya sauka suna gidajen su
Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, yace Magidanta yan gudun Hijira 500 daga Malam-Fatori, ƙaramar hukumar Abadam, za su yi azumin Ramadan a gida idan Allah ya so.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai wata ziyara yankin ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin Borno ta fitar a shafin Facebook.
Tun a farkon faruwar matsalar ayyukan ta'addancin ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2014 mafi yawan mutanen garin Malam-Fatori suka bar gidajen su.
Yayin ziyarar da ya kai, gwamna Zulum ya duba gidajen wucin gadi 100 da magidantan ke amfani da su, kafin gwamnati ta kammala gyara musu gidajen su.
A jawabinsa, Zulum ya ce:
"Magidanta 500 da Izinin Allah za su dawo gida kafin watan Azumin Ramadana. Wannan ne lokacin da ya fi dacewa mu dawo da su gida cikin kwanciyar hankali kafin ruwa ya sauka."
Gwamnan ya kuma ba da umarni ga ma'aikatar gyara da maida yan gudun hijira gida ta kammala ginin azuzuwa 5 na Firamare a yankin cikin kwanaki 10 masu zuwa.
Haka nan ya ba da umarnin a gyara Asibiti da kuma Masallacin Jumu'a dake kusa da tsohuwar kasuwar garin.
Zamu tallafa wa Magidanta da kudi - Zulum
Gwamna Zulum ya ƙara da cewa kowane Magidanci da za'a dawo da shi gida, zai samu tallafin N100,000 a wani bangare na taimaka masa ya sake gina kansa.
A wani labarin na daban kuma Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina
Jarumin Kannywood , Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.
Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng