Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

  • A yau ne kwamitin riko na jam'iyyar APC ya shaida samun sabon shugaba, inda gwamnan Neja ya maye gurbin Buni
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnan na Neja aka ruwaito ya shiga taro da wasu jiga-jigan APC
  • A wannan rahoton an bayyana batutuwan da suke da alaka da juna, har ya kai ga zaman gwamna Bello shugaba

FCT, Abuja - A ranar Litinin ne Gwamna Sani Bello na Jihar Neja ya karbe ragamar mulkin jam’iyyar APC mai mulki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya dale ragamar ne yayin da shugabancin jam’iyyar ke adawa da Gwamna Mai Mala Buni wanda ya hau kujerar shugabancin jam'iyyar na rikon kwarya a 2020.

Jim kadan da karbar ragamar mulki, Bello ya samu rahoton kwamitin shiyya na jam’iyyar gabanin taron gangamin APC da ke tafe nan gaba.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Gwamnan Neja ya zama shugaban kwamitin riko na APC
Tuna baya: Abubuwan da suka faru har gwamna Bello ya maye gurbin Mai Mala Buni | Hoto: @GboyegaAkosile
Asali: Twitter

A wata hira da manema labarai bayan zama shugaba, gwamnan na Neja ya ce rawar da ya taka a sakatariyar jam’iyyar ta kasa ya samu tofin albarka daga bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A watan jiya ne Bello ya nuna goyon bayansa ga tsayawar takarar jagoran APC na kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu dai kamar yadda batutuwa suka kankama na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da ke neman ya gaji kujerar Buhari.

Da yake jawabi a lokacin da ya tarbi Tinubu a gidan gwamnatin jihar Neja, gwamnan ya bayyana Tinubu a matsayin dan takarar da ya cancanta.

Ya ce yana fatan ganin Tinubu ya kafa irin ginshikin da ya shimfida a jihar Legas sadda yake gwamna domin kawo gagarumin sauyi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

A cewar Bello:

“Lagos kasa ce a cikin kasa kuma mun ga ginshikin da ka kafa a can. Muna sa ran ganin kwatankwacin haka ga Najeriya.”

Tattaunawar Bello da manema labarai

Bayan fitowarsa a taron da aka sanar da zamansa shugaban kwamitin riko na APC, Gwamna Bello ya yi gajeruwar tattaunawa da manema labarai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Da aka tambaye shi ko wane dalili ne yasa ya jagoranci taron na APC, Bello ya ce:

“Shugaban riko. Na jima ina aiki tun da shugaban ya yi tafiya”.

Daga nan ne wannan tattaunawa ta gudana tsakanin manema labarai da Gwamna Bello kamar haka:

Manema labarai:

"Ko za ka iya tabbatar da labarin an nada ka a matsayin shugaban riko, inda ka karbi ragamar mulki daga hannun Buni?"

Gwamna Bello ya amsa da cewa:

"Ka ce labari. Ka ce labari

Manema labarai:

"Amma muna bukatar mu ji daga bakinka?"

Kara karanta wannan

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

Gwamna Bello:

"Babu wani tsokaci."

Amma to, shin gajeren zangon mulkin APC na Bello (yana da har zuwa ranar 26 ga Maris) ka iya fassara wani abu mai kyau ga kamfen na shugabancin Tinubu?

Kwamitin raba mukamai ya mika rahoto ga sabon shugaban APC na kasa

A wani labarin, kwamitin tsarin karba-karba ya mika rahoton tsara jadawalin raba mukamai ga sabon shugaban rikon kwarya na APC, gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ranar Litinin a Abuja.

Sakataren watsa labarai na gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas, Gboyega Akosile, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, shi ne ya mika rahoton ga kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.