Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1
- Wani magidanci da ya yi fice a shafukan soshiyal midiya a bara sakamakon auren mata biyu a rana daya ya yi murnar cikarsu shekara guda da aure
- Babangida Adamu ya fita shakatawa da matan nasa domin tunawa da wannan rana a jiya Lahadi, 6 ga watan Maris
- Aure dai ya yi albarka domin an samu haihuwar da daya yayin da dayar matar ke dauke da tsohon ciki
Masu iya magana kan ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a kaiba. Tafiya dai ta fara mika tsakanin wani magidanci da ya auri mata biyu a rana daya.
A bara ne dai labarin mutumin mai suna Babangida Adamu Sadiq, ya karade shafukan soshiyal midiya sakamakon auren mata biyu, Maimuna Mahmud da Maryam Muhammad Na'ibi da ya yi a rana daya.
A ranar 6 ga watan Maris din 2021 ne dai aka daura auren masoyan. Don a haka ya shirya bikin murnar zagayowar wannan rana a jiya Lahadi.
Aure ya yi albarka, an samu 'karuwa
Mahmud dai ya fita shakatawa tare da matan nasa don karrama rana kuma tuni aure ya yi albarka har an samu haihuwar da daya.
A hotunan murnar zagayowar ranar wacce jaridar Punch ta wallafa, an gano daya matar dauke da tsohon ciki wanda yake nuna haihuwa ko yau ko gobe.
Sannan alamu sun nuna ana zaman lafiya tsakanin matan duba ga yadda dukkansu suke dauke da farin ciki da walwala a fuskokinsu.
Kamar yadda shafin Linda Ikeji ta rahoto, Babangida ya yi wani wallafa kan wannan rana inda ya ce:
"Alhamdulillah. Alhamdulillah. Alhamdulillah. zukata Nagartattun zukata ne kawai za su iya samar da irin wannan haduwar, Ina godiya ga Allah da samun irin wadannan mata a rayuwata. Barka da zagayowar ranar aurenmu ya ku matana abin kaunata. 6/3/2022."
Dan shekara 21 nake son aure: Yar shekara 70 da bata taba aure ba, bata taba sanin namiji ba
A wani labarin, wata mata yar shekara 70 mai suna Genevieve wacce bata taba aure ba ko saurayi ko sanin namjiji ba ta bayyana irin namijin da take so.
Genevieve na fama da nakasar kafa wanda ke hanata tafiya.
A hirar da tayi da Afrimax, matar ta bayyana cewa ba haka aka haifeta ba a shekarar 1952. Amma daga baya iyayenta suka gani bata iya tafiya sai da rarrafe.
Asali: Legit.ng