Shehu Sani ya bayyana abun da Obasanjo ya fada masa lokacin da aka yanke masu hukuncin daurin rai da rai
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, sun yi zaman gidan yari a tare a shekarun baya
- Sani ya tuna yadda alkalin kotun soji ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai da kuma shekaru bakwai a gidan yari kan cin amanar kasa
- Dan majalisar na Kaduna ya ce Obasanjo ya tambaye shi wanne daga cikin hukuncin zai fara yi
Tsohon dan majalisa wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya yi waiwaye kan lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai tare da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, tsohon sanatan ya tuna da kalaman da Obasanjo ya yi a wancan lokacin.
Ya ce a wancan lokacin, Obasanjo ya yi masa tambaya kan wanne daga cikin hukuncin zai fara yin a daurin rai da rai ko kuma na shekaru bakwai da aka yanke masa.
Ya rubuta:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Lokacin da alkalin kotun sojoji a Lagas ya yankewa Obj daurin rai da rai kan cin amanar kasa sannan aka yanke mana ni da Dr Beko hukuncin daurin rai da rai da kuma Karin shekaru 7 kan cin amanar kasa, Obj ya juya ya kalle ni sannan ya tambayeni matashi, wanne z aka fara da shi, shekaru 7 a gidan yari ko daurin rai da rai?"
An kama Obasanjo ne a shekarar 1995, sannan daga baya aka kuma yanke masa hukunci bisa zarginsa da hannu a juyin mulki.
Shima Shehu Sani gwamnatin soji ta kama shi sannan ta yanke masa hukuncin dauri.
Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo
A gefe guda, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, ya ce da ace hukumar EFCC na aikinta yadda ya kamata toh da ya kamata ace wasu masu neman takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023 suna a gidan yari.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na bikin cikarsa shekaru 85 a Abeokuta, babban birninjihar Ogun, jaridar Punch ta rahoto.
Tsohon shugaban kasar ya ce koda dai masu neman takarar shugaban kasa da dama sun ziyarce shi domin neman goyon bayansa, shi bai tsayar da wani dan takara da zai marawa baya ba.
Asali: Legit.ng