N56,000 za mu baku: FG za ta raba wa wadanda suka dawo daga Ukraine kudin kashewa
- Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kwaso 'yan Najeriya da suka makale a kasare Ukraine yayin da yaki ya barke
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar soja a kasar Ukraine
- Gwamnatin Najeriya ta fara jigilar kwaso 'yan Najeriyan da suka fake a wasu kasashen da ke kusa da Ukraine
FCT, Abuja - Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce karin jirage guda biyu da ke kwashe ‘yan Najeriya daga kasar Ukraine za su iso a yau dinnan.
Kashi na farko na 'yan Najeriya da suka tsere daga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sun iso Abuja da safiyar yau Juma'a.
‘Yan Najeriya 411 da suka hada da dalibai da ma’aikatan ofishin jakadanci sun isa filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da safiyar yau.
Da take mayar da martani ga ci gaban, shugabar NiDCOM ta ce
"Godiya ta tabbata ga Allah jirgin Max Air VM602 mai kwaso mutane daga Bucharest ya sauka a Abuja."
Ta kara da cewa wadanda za a kwaso sun kai 416 sabanin 411 da aka ruwaito a baya.
Hakazalika, Vanguard ta ruwaito cewa, duk wanda ya dawo za a bashi dala 100 kwatankwacin Naira 56,000 daga Gwamnatin Tarayya idan ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.
A cewar karamin ministan harkokin wajen kasar, Ambasada Zubairu Dada, kasashen da za a fara jigilar jiragen don kwaso 'yan Najeriya sun hada da Poland, Hungary, Slovakia, da Romania.
Baya ga ba da kyautar kudi, gwamnatin Najeriya ta cire kudin gwajin Korona akan duk wadanda aka kwaso daga kasar ta Ukraine, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kamfanin Google ya sanya wa Rasha takunkumi mai tsanani
Kamfanin fasaha na Google a Amurka kuma katafaren dandalin bincike na yanar gizo, ya dakatar da duk wani nau'i talle da 'yan Rasha ke yi, a daidai lokacin da Shugaba Vladimir Putin ya fara yakar kasar Ukraine.
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa Google ya sanar da dakatarwar ne a daren jiya Alhamis 3 ga watan Maris.
Legit.ng ta tattaro cewa kamfanin ya dauki wannan mataki ne bayan da hukumar kula da harkokin intanet ta kasar Rasha ta umarce shi da ya daina nuna tallace-tallacen da suke nuna bayanan karya game da mamayar kasar Ukraine.
Asali: Legit.ng