Ko gizau: Yadda Elon Musk ya yi asarar kwatankwacin dukiyar Dangote sau 3 a 2022

Ko gizau: Yadda Elon Musk ya yi asarar kwatankwacin dukiyar Dangote sau 3 a 2022

  • Elon Musk ya ga faduwa a yawan dukiyarsa cikin watanni biyu da suka gabata na 2022 bayan da kamfanin motarsa ya gaza samun ciniki mai yawa a kasuwa
  • Musk ya yi asarar kwatankwacin dukiyar hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote sau uku, duk da lamurran da kamfanin simintin Dangote ke fuskanta
  • Mai kamfanin na mota Tesla ya yi asarar kusan dala biliyan 35 a bana kadai, yayin da dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 20

Duk da dukiyar da Dangote ke da shi a matsayinsa na attajirin da ya fi kowa duniya a Afirka, ba ya ko kusa mai kamfanin Tesla da SpaceX, Elon Musk wanda ya yi nisan nisa, shi ke kan matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya.

Elon Musk ya yi asara a cikin watanni biyun da suka shude, adadin da aka ce ya kai kwatankwacin dukiyar Aliko Dangote sau uku, sakamakon tabarbarewar da Tesla ya samu, kamfanin mota mafi daraja a duniya.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

Aliko Dangote bai kai ko kusa da Elon Musk ba
Daram: Yadda Elon Musk ya yi asarar kwatankwacin dukiyar Dangote sau 3 a 2022 | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Dukiyar Elon Musk da rashin da ya yi

Kamfanin kera motoci masu amfani da wutar lantarki na Tesla ya yi asarar dala biliyan 48.4 tun farkon 2022, in ji rahoton Bloomberg's Billionaire Index.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dukiyar Elon Musk yanzu ta kai dala biliyan 222.

Kididdigar Bloomberg, ta nuna cewa dukiyar Dangote ya kai dala biliyan 20, kusan ninki uku kuma fiye da ninki biyu na dukiyar da attajirin da ya fi kowa dukiya a duniya ya yi hasarar ta a 2022.

Wani rahoto na Nairametrics ya ce dukiyar Elon Musk za ta iya sayen tubalin zinari miliyan 113 da ganga biliyan 2 na danyen mai.

Kamfanin motarsa, Tesla ya kai wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba a ranar 4 ga Nuwamba, 2021, lokacin da dukiyar Elon Musk ta kai dala biliyan 340.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan da ya tambayi mabiyansa a shafin Twitter ko dai ya sayar da wasu hannayen jarinsa, daga nan ne hajar kamfanin ta yi kasa sosai, inda ta zubar da dala biliyan 35 daga dukiyarsa a rana guda. Rashi ne da bai taba yin irinsa ba.

Mai kyauta kuma mai taimakon jama'a

Elon Musk ya ba da hannun jarin da ya kai dala biliyan 5.7 yayin da ya kammala siyar da hannayen jarin da suka haura dala biliyan 16.

Kamfanin motarsa, Tesla ya yi hasarar dala tiriliyan 1 na tsohuwar kimarta ta kasuwa duk da ya kera adadin motoci masu yawa a bara.

Duk da tarihin Aliko Dangote sau 11 na kasancewa mutumin da ya fi kowa dukiya a Afirka, a cewar rahoton Forbes, Elon Musk ya nuna cewa asarar kusan ninki uku na dukiyar Dangote ba zai shafi komai ba a rayuwarsa.

Baje kolin Kaduna: Kamfanin takin Dangote zai gudanar da shiri tsakaninsa da manoma

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

A wani labarin, wani rahoton Daily Trust ya ce, kamfanin taki na Dangote zai gudanar da shiri na musamman don taimakawa maonma da kwastomomi a yayin bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa da za ake gudunarwa a Kaduna.

Shirin na teburin tattaunawa da warware matsalolin kwastomomi da manoma zai gudana ne a yayin bikin baje kolin kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Sanarwar da Sashen Sadarwa na kamfanin ya fitar ta ce baya ga kayayyakin takin da ake sayar da su a kan farashi mai sauki tare da fakiti na musamman ga manoma, ana kuma ba da kyaututtuka ga kwastomomi a yayin baje kolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.