An Ba Wa Mele Kyari Wa’adin Kwana 7 Ya Kawo Karshen Ƙarancin Man Fetur a Najeriya

An Ba Wa Mele Kyari Wa’adin Kwana 7 Ya Kawo Karshen Ƙarancin Man Fetur a Najeriya

  • Kungiyar 'The Citizens Awareness Against Corruption and Social Vices Initiative' ta bawa Mele Kyari wa'adin kawo karshen karancin man fetur
  • Kungiyar cikin wata wasika da a aike wa shugaban na NNPC ta ce idan bai kawo karshen matsalar cikin kwana 7 ba za ta bukaci Buhari ya sallame shi
  • A cewar kungiyar, kananan laifuka sun karu da kashi 40 cikin 100 a jihohin Najeriya 36 da Abuja saboda jami'an tsaro suna bata lokaci a gidan mai a maimakon yin aikinsu

Wata kungiya mai yaki da rashawa da wayar da kan al'umma 'The Citizens Awareness Against Corruption and Social Vices Initiative' ta bawa shugaban NNPC, Mele Kyari, wa'adi ya kawo karshen karancin man fetur.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata na 3 ga watan Maris da direktan YTLC, Olumuyiwa Onlede ya saka wa hannu, kungiyar ta sha alwashin za ta bukaci Kyari ya yi murabus idan bai saurari gargadinsu ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa

An Ba Wa Mele Kyari Wa’adin Kwana 7 Ya Kawo Karshen Ƙarancin Man Fetur a Najeriya
Kungiya Ta Ba Wa Mele Kyari Wa’adin Kwana 7 Ya Kawo Karshen Ƙarancin Man Fetur a Najeriya. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

A cewar kungiyar, wa'adin ya zama dole ne domin saukaka wa yan Najeriya mawuyacin halin da suka shiga saboda layun mai da suka ki karewa tsawon makonni, rahoton Daily Nigerian.

Wani sashi na wasikar ya ce:

"Matakin da muka dauka shine baka wa'adin kwana 7 ka magance matsalar karancin man fetur idan ba haka ba, ba mu da zabi sai dai shawartar shugaban kasa ya sallame ka daga aiki."

Kungiyar ta koka cewa tsawon wata biyu an mayar da Najeriya baya zamanin kama karya na soja inda suke bata lokacinsu a gidajen mai don zuba wa a ababen hawansu.

Kungiyar ta ce karancin man fetur ya janyo karuwar kananan laifuka a kasa

"Binciken da muka yi a jihohi 36 da Abuja ya nuna kashi 40 cikin 100 na motoccin jami'an tsaro musamman yan sanda suna bata lokacinsu suna layin mai hakan ya kan hana su aikinsu.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

"Lamarin ya janyo karuwar kananan laifuka da kashi 20 cikin 100 kuma hakan saboda sakacin NNPC ne na gaza yin tunani mai kyau na samarwa jami'an tsaro mai ba tare da sun bata lokaci ba," a cewar sanarwar.

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

A baya, kun ji cewa babban manajan darektan hukumar NNPC, Mele Kyari ya ce rarraba man fetur zai tabbata cikin makwanni kadan masu zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Manajan ya ce zuwa karshen wannan watan za a rarraba Lita miliyan 2.1 na man fetur don ya yalwatu a kasar nan.

Kyari ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wani taro da kwamitin rikon kwarya ta majalisar wakilar wacce take bincike dangane da gurbataccen man fetur din da aka shigo da shi kasar nan kamar yadda Vanguard ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164