Jerin Kasashen Afirka 17 da suka yarda su jefa Kuri'ar Allah wadai da Rasha
- Yayin da yaƙin Rasha da Ukraniya ya shiga rana ta takwas, kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da lamarin
- Zauren majalisar dinkin duniya ya gudanar da kuri'ar ra'ayi, kasashe 17 daga Afirka sun ki kaɗa kuri'ar Allah wadai da Rasha
- Tuni gwamnatin Najeriya ta yi kira ga Rasha ta gaggauta fitar da sojojinta daga ƙasar Ukraniya, yau lamarin ya shiga rana ta 8
Wasu kasashe guda 17 a nahiyar Afirka sun ƙi yarda su jefa kuri'ar yin Allah wadai da hare-haren da Rasha ta jaddamar kan ƙasar Ukraine a taron majalisar dinkin duniya (MDD).
BBC Hausa ta tattaro cewa kasashen sun kauce wa lamarin ba tare da ɗaukar matsaya ba kan yin Allah wadai da lamarin ko kuma akasin haka a taron MDD.
Jerin ƙasashen sun haɗa da Afirka ta Kudu, Aljeriya, Uganda, Burundi, Mozambique, Mali, Sudan ta Kudu da kuma Senegal.
Sauran ƙasashen da suka kauce wa lamarin su ne, Congo, Tanzaniya, Madagaskar, Equatorial Guinea, jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Angola, Sudan, Nambia da Zimbabwe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kazalika an samu ƙasa ɗaya daga nahiyar Afirka da ta kaɗa kuri'ar kin amincewa da matakin yin Allah wadai da mamayar Rasha, kuma ƙasar ita ce Eritrea.
Ƙasar Uganda ta bayyana cewa ta ɗauki matakin kin shiga lamarin ne saboda ta tabbatar da matsayin na, "Yar ba ruwa na."
Haka nan ƙasar ta ce ta yi haka ne a kokarin da take na zama shugaban gamayyar ƙasashen yan ba ruwan mu (NAM).
Tuni dai Najeriya ta yi Allah wadai da matakin Rasha tare da yin kira gareta ta gaggauta janye sojojinta daga kasar Ukraine.
A halin yanzun, gwamnatin tarayyan Najeriya na ta faɗi tashin ganin ta kwaso yan kasarta da yaƙin ya rutsa da su a Ukraniya.
Matar Tanko ta ba da shaida a Kotu
A wani labarin kuma Matar makashin Hanifa Abubakar ta juya masa baya a Kotu, ta faɗi gaskiyar lamari
Matar wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a Kotu bayan ya ce ba shi ya kashe ta ba.
Jamila ta faɗi yadda ya kawo mata yarinyar da kuma karyar da ya mata game da ita, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare bayan kwana 5.
Asali: Legit.ng