Zanga-zanga: Mata sun tare kofar majalisa saboda kin amincewa da wani kudirin mata
- A yanzu haka kungiyoyin mata na nan sun tare kofar majalisar dokokin tarayya da ke Abuja
- Matan na zanga-zanga ne a kan kin amincewa da kudirin samar da kujeru na musamman ga mata a majalisun tarayya da na jiha
- Sai dai jami'an tsaro sun hana su shiga harabar majalisar, inda su kuma suka ce lallai sai sun san yadda kowani dan majalisa ya kada kuri'a
Abuja - Kungiyoyin mata daban-daban sun toshe kofar shiga sakatariyar majalisar dokokin tarayya domin yin zanga-zanga a kan sakamakon zaben da aka yi na gyaran kundin tsarin mulkin kasar.
Jami’an tsaro basu bari matan da ke zanga-zangar sun samu shiga cikin harabar majalisar dokokin ba, inda suka rufe su a waje, jaridar The Nation ta rahoto.
A yayin da suke kada kuri’a a majalisar dokoki a ranar Litinin, an yi watsi da kudirin da ke neman a inganta ra’ayin mata.
Kudirin dai ya nemi a samawa mata kujeru na musamman a majalisar dokoki, majalisar jiha, da kuma kaso 35 na shugabancin jam’iyya.
Matan sun nace cewa lallai ba za su bar wajen ba har sai sun gana da shugabancin majalisar dokokin kasar.
Har zuwa lokacin kawo wannan rahoton, kofar majalisar na nan a rufe.
Rahoton ya kara da cewa matan sun ce ya zama dole su san yadda kowani dan majalisa ya kada kuri’a.
Majalisun tarayya sun yi watsi da kudurin ware wa mata Kujeru, da kudirin VAT
A baya mun kawo cewa majalisar tarayya a Najeriya ta yi fatali da kudirin samar da kujeru na musamman ga mata da kuma na canza wa biyan harajin VAT wuri zuwa jerin Waje.
Daily Trust ta rahoto cewa mambobin majalisar sun yi watsi da kudirorin biyu ne yayin kaɗa kuri'a kan abubuwa 68 da aka maida hankali wurin gyaran kwansutushin, ranar Talata.
A majalisar wakilan tarayya, Mambobi 209 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa da canza wa VAT wuri, yayin da mambobi 208 suka ki amincewa da ware wa mata kujeru na musamman.
Asali: Legit.ng