Sabon jidali: Tallafin mai zai karu kan FG yayin da farashin mai ya tashi zuwa $112.7 kan kowacce ganga
- Farashin mai na ci gaba da tashi a duniya sakamakon yakin da ya dumfaro tsakanin Rasha da Ukraine
- Farashin mai ya kai dalar Amurka 112.70 a wannan karon, mafi girma kusan shekaru 11 da suka gabata
- Wannan na nufin, gwamnatin Najeriya za ta kara kashe kudade wajen samar da tallafin man fetur ga 'yan kasar
Farashin danyen mai ya ba da mamaki a kasuwannin duniya a ranar Talata, inda aka sayar da ganga daya sama da dalar Amurka 110 a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici tun bayan da Rasha ta yi kokarin mamaye Ukraine.
Tashin farashin na nufin karin kudaden tallafi ga gwamnatin Najeriya domin a sayar da man fetur a farashi kasa da na kasuwannin duniya, TheCbale ta ruwaito.
Wannan ci gaban na zuwa ne duk da cewa Amurka da sauran kasashen mambobin Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) sun amince da sakin ganga miliyan 60 da suka adana na man fetur don daidaita farashin mai a duniya.
A jiya, danyen mai na Brent ya haura zuwa sama da 7.80% daidai da dalar Amurka 112.70 kan kowace ganga - kusan karin dala 8 a kowace ganga kenan daga ranar Talata, kana tashi mafi girma tun watan Fabrairun 2011, akalla shekaru 11.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar OPEC da kawayenta za su gana a yau Laraba don tattaunawa mai mahimmanci kan fitar wata-wata na mai na Afrilun 2022.
A watan Janairu, Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya yi ikirarin kashe Naira biliyan 210.38 na tallafin mai., kamar yadda The Street Journal ta tattaro.
A cikin watan, kamfanin man bai saka kudi a asusun tarayya ba, matakin da ka iya haifar da gazawar gwamnatocin jihohi wajen biyan albashi.
Haka kuma ta ware Naira biliyan 242.5 daga kudaden shiga na gwamnatoci a watan Fabrairu.
Kimanin Naira biliyan 143.7 daga cikin Naira biliyan 242.5 da aka ware, an ce za a yi amfani dasu ne wajen farfadowar watan Janairun 2022 da kuma biyan bashin watan Nuwamban bara na Naira biliyan 98.8.
A watan da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince da kasafin Naira tiriliyan 2.557 na tallafin man fetur a 2022.
Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa
A wani labarin, wani rahoton jaridar Punch ya kawo cewa gwamnatin tarayya ta hukumar kula da man fetur na iya mayarwa masu kawo mata mai daga kasar waje gurbataccen man fetur da kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ta shigo da shi kasar.
Masu siyar da mai sun kiyasta cewa kimanin lita miliyan 100 na gurbataccen man fetur aka shigo da su Najeriya, kuma kamfanin sayar da kayayyakin bututun mai, wani bangare na NNPC ya janye shi.
A rahoton Vanguard, hukumar NMDPRA ta bayyana cewa gwamnati ta janye kimanin lita miliyan 80 na gurbataccen man daga kasuwar cikin gida.
Asali: Legit.ng