Niger: 'Yan ta'adda sun ragargaza garinsu sakataren gwamnatin jihar
- 'Yan bindiga sun shiga garin Matane, garinsu sakataren gwamnatin jihar Niger inda suka tarwatsa mutanen garin
- Ganau sun tabbatar da cewa sun kutsa ranar Talata wurin karfe 5 na yammaci kuma suka dinga kone shaguna, gidaje da kadarori
- An gano cewa sun shiga kauyen Bamba-Lamba inda suka dinga ragargazar jama'a duk da har yanzu ba a san yawan wadanda suka halaka ba
Niger - 'Yan ta'adda sun gigita kauyen Matane, garinsu sakataren gwamnatin jihar Niger, Alhemd Ibrahim Matane.
Kauyen yana nan a karamar hukumar Mashegu ta jihar Niger kuma ya fuskanci hare-hare marasa adadi a cikin kwanakin nan, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta tattaro cewa, miyagun sun kutsa kauyen a ranar Talata inda suka dinga babbaka shaguna, gidaje da kadarorin jama'a.
Maharan sun kara da kutsawa yankin Bamba-Lamba da ke da nisan kilomita kadan zuwa gabashin Kontagora.
Wani mazaunin Bamba-Lamba, Hashimu Ahmed, ya sanar da manema labari cewa miyagun sun shiga yankinsu wurin karfe 5 na yamma kuma sun dinga kone wurare.
"Sun zagaye yankin baki daya. Da kyar na samu na tsere zuwa Kontagora da iyalina. Sun kone mana gidaje. A yanzu haka a kango muke kwana, muna bukatar taimako," yace.
Kwamishinan kananan hukumomi da tsaron cikin gida na jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar da aukuwar farmakin.
Ya ce gidaje masu tarin yawa da shaguna tare da kadarori duk sun ci wuta. Umar ya ce bai tabbatar da yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa, maharan sun dinga shiga kauye bayan kauye amma jami'an tsaro sun dinga bibiyar sahun 'yan bindigan tun ranar Litiniin yayin da suka rufe babban titin Minna zuwa Suleja.
Ya ce 'yan bindigan sun fusata saboda hanyar tserewarsu Zamfara ce kadai kuma sojoji sun toshe ta.
Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa
A wani labari na daban, a kalla rayuka 17 da suka hada da uba da dansa wasu miyagun 'yan ta'adda suka halaka a kauyukan kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi dake jihar Niger.
Jama'a da yawa sun dinga barin gidajensu sakamakon farmakin wanda ya auku daga karfe 12 na rana zuwa karfe takwas na ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.
A karamar hukumar Mashegu, kauyukan da aka kai hari sun hada da Sabon-Rami, Igbede, Chekaku, Ubegi, Maishankafi da Poshi.
Babban sakataren yada labarai na shugaban karamar hukumar Mashegu, Mohammed A. Isah, ya sanar da manema labarai cewa shugaban ma'aikatan gwamnatin karamar hukumar, Umar Ubegi da mahaifinsa duk sun rasa rayukansu yayin farmakin.
Asali: Legit.ng