Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki
- Wasu mata biyu sun hadu da ajalinsu a hannun yan bindiga yayin da suke a hanyarsu ta zuwa wani biki a Abuja
- Maharan sun budewa motar da suke ciki wanda ya baro yankin Abaji wuta a daidai kauyen Ukya-Tsoho, da ke yankin Kuje
- An tattaro cewa yan bindigar sun fito ne daga wani daji da ke kwanar kauyen
Abuja - Yan bindiga sun kashe wasu mata biyu, Safiya Salihu da Amina Ibrahim, a hanyarsu ta zuwa wajen wani bikin aure.
Maharan sun budewa motarsu wuta a kauyen Ukya-Tsoho, da ke yankin Kuje na babbar birnin tarayya Abuja.
Wani direba, wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Abdullahi, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Juma’a, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya ce yan bindigar sun fito ta daji a wani kwana yan mita kadan daga kauyen Ukya-Tsoho sannan suka bude wuta kan wata motar Volkswagen Golf mai lamba LKJ 321 CX.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wasu yan biki biyu da aka kashe sun shiga mota ne daga Abaji a hanyarsu ta karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa domin halartan biki.
Ya ce:
“Ina yan mita kadan a bayan motar saboda dukkanmu mu biyun mun dauko fasinjoji ne daga Abaji. Da muke kokarin kwana a kusa da Ukya-Tsoho, sai yan bindigar suka bayyana sannan suka fara harbin motar.”
Direban ya ce yana jin karar harbi, sai ya saka birki sannan ya yi gaggawan juya kan motarsa domin tsira daga harin, inda ya ce direban motar da ke dauke da mamatan ya yi nasarar tserewa duk da ruwan harsashi da aka yiwa motarsa.
Rahoton ya kuma ce an kwashi gawawwakin mamatan zuwa Gegu a karamar hukumar Kotonkafe da ke jihar Kogi domin binnewa.
Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ba kan lamarin.
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun sace amarya tare da hallaka mutum 8 a Neja
A wani labari, Yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja.
An tattaro cewar yan bindigar sun kai hari wajen wani taro na aure sannan suka sace amarya. Sun kuma kashe mutane takwas sannan suka jikkata wasu da dama.
Garuruwan da aka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu, rahoton Arise tv.
Asali: Legit.ng