Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba
- Kotun da ke zama a babban binrin tarayya Abuja ta yi watsi da neman ba da belin Abba Kyari da aka tsare
- Idan baku manta ba an tsare Kyari ne bisa zarginsa da harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa inji NDLEA
- Ya kai kara kotu, ya ce an take hakkinsa kuma yana neman beli domin ya je ya yi jinyar rashin lafiyar da ke damunsa
FCT, Abuja - Rahotanni daga wata babbar kotun tarayya da ke Abuja sun ce, kotun ta ki bayar da belin DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar (DCP) bisa wasu tuhume-tuhume.
The Cable ta ruwaito cewa, mai shari'a Inyang Ekwo, ya yanke hukunci a ranar Litinin, cewa bukatun da aka bijiro dasu sun wuce gona da iri.
Idan baku manta ba, a ranar 14 ga Fabrairu, hukumar NDLEA ta bayyana cewa ana neman Kyari bisa “hannu a harkallar hodar iblis mai nauyin kilogiram 25”.
Sa’o’i kadan bayan haka, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kama shi tare da mika shi ga hannun hukumar NDLEA.
Kyari ya shigar da karar gwamnatin tarayya a gaban kotu inda ya kalubalanci zargin safarar miyagun kwayoyi da ake yi masa, kana ya ce ba komai bane face shirme.
A watan Fabrairu, ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abuja domin neman belinsa bisa dalilan rashin lafiya, inda yace yana fama da hawan jini, ciwon sukari da dai sauransu.
Alkalin kotun, ya ce zai saurari matakin da ya dace na ci gaba da tsare Kyari bayan wa’adin kwanaki 14 da kotu ta bayar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daga nan sai ya dage ci gaba har zuwa ranar 15 ga Maris don sauraron bukatar Kyari na neman a tabbatar an bi masa kadunsa.
Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6
A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar NDLEA na neman izinin ci gaba da tsare Abba Kyari da wasu mutum shida da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta bayar da umarnin a tsare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus na tsawon kwanaki 14 a cibiyar NDLEA da ke Abuja kafin a gudanar da bincike, inji rahoton The Nation.
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, ci gaba da tsare Abba Kyari da 'yan tawagarsa zai ba hukumar ta NDLEA damar ci gaba da bincike mai zurfi kan lamarinsa, kamar yadda lauyan NDLEA ya nema.
Asali: Legit.ng