Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun sace amarya tare da hallaka mutum 8 a Neja
- Wasu tsagerun yan bindiga kimanin su 100 sun kai hari wasu garuruwa a jihar Neja
- Maharan sun yi garkuwa da wata amarya a wajen taron bikinta sannan suka hallaka mutane takwas
- Kauyukan da suka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu duk a karamar hukumar Lavun ta jihar
Niger - Yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja.
An tattaro cewar yan bindigar sun kai hari wajen wani taro na aure sannan suka sace amarya. Sun kuma kashe mutane takwas sannan suka jikkata wasu da dama.
Garuruwan da aka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu, rahoton Arise tv.
Harin wanda aka fara shi a daren ranar Asabar ya kai har washegarin Lahadi inda yan bindigar suka kuma sace wasu dabbobi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kauyen Gbacitagi, yan bindigar sun farmaki taron biki, suka yi garkuwa da amarya da wata mutum daya, sannan suka yi awon gaba da kudade da wasu muhimman kayayyaki, sun kuma lalata motoci.
An rahoto cewa maharan sun kashe mutum daddaya a garuruwan Ebbo, Tsonfadagabi, Tsogi, da Kanko.
Maharan sun hadu da cikas a hanyarsu ta fita daga garuruwan tare da dosar garin Akare da ke karamar hukumar Wushishi da wasu dabbobin sata, domin gadar da ke sada garin da Akare ya karye.
Kwamishinan tsaro na jihar ya tabbatar da harin
Gidan talbijin na Channels ta rahoto cewa Kwamishinan kananan hukumomi da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, ya tabbatar da harin. Sai dai, ya ce bai samu karin bayani ba kan lamarin.
Amma mazauna yankunan, sun bayyana cewa maharan basu yi nasarar tsallake ruwan gadar da ya karye ba da dabbobin, don haka sai suka yasar da su a wajen sannan suka yanke shawarar shiga garin Shehi don samun wata hanyar fita daga garin.
Sai dai kuma, mazauna garin sun yi gaba-da-gaba da su, lamarin da ya kai ga musayar wuta a tsakaninsu da yan banga.
An tattaro cewa mutane shida aka kashe a musayar wutan wato yan banga biyu da mazauna hudu.
Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja
A wani labarin, mun kawo cewa yan ta’adda sun yi garkuwa da akalla mutane takwas a yayin da suke yin ibadah a cocin Salama Baptist Church da ke kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Wata majiya daga garin ta ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa.
Majiyar ta bayyana cewar limamin cocin na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng