NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol 649,300 a filin jirgin sama na Legas
Legas - Jami'an hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun kama a kalla kwayoyin Tramadol masu nauyin 225mg guda 649,300 da Euro809,850 da sauran miyagun kwayoyi da aka shigo dasu daga Pakistan, Australia da Italiya a titin jirgin Murtala Muhammad (MMIA) na Ikeja dake jihar Legas.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce, a ranar Lahadi a Abuja, jami'an hukumar sun kara kama sauran miyagun kwayoyin da aka shigo dasu daga Turai, America da Canada a wannan filin jirgin.
Kamar yadda ya bayyana, a kamfanin kula da sufirin jiragen sama na Skyway, ma'aikatan hukumar sun kwace kwayoyin Tramadol na 225mg guda 549,300 masu nauyin kilo 460.95 wanda aka shigo dasu daga Pakistan ta Addis Ababa ta jirgin Ethiopia a ranar 16 ga watan Fabrairu, tare da kama wani wanda ake zargi, Nwadu Ekene Christian.
A wannan ranar, an kama wata fasinja mace, Ms Ayeki Happy, wacce ta isa filin jirgin daga Italy a jirgin Turkish da Euro 69,850 da ta boye a kayan ta.
Wannan yazo ne, bayan kwana hudu da kama wata mata, Precious Idahagbon da Euro740,000 da ta boye a akwatin ta, sannan ba wanda ya san lokacin da ta isa filin jirgin daga Vienna, Australia ta Istanbul, Turkey.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ana cigaba da bincika kudaden da aka kwacen don tabbatar da ba ta safarar miyagun kwayoyin aka same su ba," a cewar Babafemi.
A Kano, an kama wani matashi mai shekaru 34, Nasiru Abdulrahman da wiwi mai nauyin kilo 476 a kwanar Dan gora dake karamar hukumar Kiru na jihar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Inda a Adamawa, aka kama Abdulmuminu Abubakar, mai shekaru 24 da 225mg na Tramadol, a Gidan Madar a arewancin karamar hukumar Mubi a ranar 22 ga watan Fabrairu, kan babur a hanyar shi ta safarar miyagun kwayoyin zuwa Bukula dake Jamhuriyar Kamaru.
Abubukar yayi ikirarin cewa, wani wanda ake zargi, Fahad Mohammed, mai shekaru 19 ya bashi miyagun abububan. Daga baya aka kama Fahad a gidansa cikin Kasuwan yankin Borkono a cikin garin Mubi.
NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi
A wani labari naa daban, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu kudin jabu a tsabarsu da suka kai $4.7 miliyan a Abuja.
A wata takarda da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce jami'an hukumar a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 18 ga watan Fabrairu sun tsare wasu kaya da aka aiko daga Legas zuwa Abuja a yankin Abaji da ke babban birnin tarayya.
Kamar yadda Babafemi yace, kama kudin jabun ya yi sanadin da aka damke babban wanda ake zargi mai shekaru 52 mai suna Abdulmumini Maikasuwa.
Asali: Legit.ng