Da Ɗuminsa: Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno

Da Ɗuminsa: Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno

  • Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne ko kuma ‘yan ISWAP sun kara kai farmaki karamar hukumar Chibok da ke Jihar Borno
  • Sakamakon farmakin, sun halaka dan wani dagacin kauye, Bulama Wadir da wasu ‘yan gudun hijira wadanda ke zama a kauyen guda biyu
  • Wannan farmakin ya biyo bayan wani da suka kai a watan Janairu wanda suka yi garkuwa da fiye da mutane 10, wanda harin ya fi shafar yara da mata

Borno - Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun kara kai hari kauyen Kautikari da ke karkashin karamar hukumar Chibok inda suka halaka dan dagacin kauyen, Bulama Wadir da wasu ‘yan gudun hijira biyu da ke garin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dumfaro kauyuka a Filato, hakimai na ta kansu

Babu nisa sosai tsakanin kauyen Kautikari da garin Chibok, kuma harin ya auku ne bayan wani kazamin farmaki da suka kai a watan Janairun 2022 wanda suka yi garkuwa da fiye da mutane 10 yawanci mata da yara.

Da Ɗuminsa: Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno
Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira 2 Chibok. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Sun banka wuta a coci mafi girma da ke makwabtaka da dajin Sambisa.

Farmakin yana kara yawaita a kauyen Kautikari, Pemi, Korohuma da sauran kauyaku da ke zagaye da Chibok tun watan Janairun wannan shekarar.

Gwamnan jihar Borno ya kai wa 'yan Chibok ziyara

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya kai ziyara Chibok a ranar 14 ga watan Janairu don nuna tausayi da kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati za ta tabbatar ta kula da rayuwar mazauna garin.

Idan ba a manta ba, gwamnan ya je har wurin ‘yan uwan mata 22 da maza 2 da mayakan ISWAP/ Boko Haram suka sace a hare-hare daban-daban.

Kara karanta wannan

Ana yunkurin kawo doka saboda manyan majalisa su rika karbar fansho har su mutu

Zulum ya gayyaci ‘yan uwan wadanda harin ya ritsa da su har gidan gwamnati da ke garin Chibok.

Mazauna yankin sun sanar da wakilin Vanguard cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:45 na yammacin ranar Juma’a, sai dai saboda rashin kafar sadarwa manema labarai basu sani ba.

Kamar yadda majiyoyin suka shaida:

“An kai wa anguwar mu farmaki da yamman nan da misalin karfe 5:45 na yamma. Maharan sun babbake wasu coci-coci da gidajen cocin Brethren, Ekliziyan Yan’uwa a Najeriya, wacce aka fi sani da E.Y.N inda suka halaka dan dagacin kauye, Bulama Wadir.”

Wani mazaunin yankin, John Usman ya sanar da wakilin Vanguard ta wayar salula a ranar Juma’a cewa:

“In banda rundunar soji ta kai dauki, da maharan sun halaka gabadaya mazauna yankin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164