'Yan bindiga sun sace ma'aurata a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama, sun kashe 'yan sanda dake raka su

'Yan bindiga sun sace ma'aurata a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama, sun kashe 'yan sanda dake raka su

  • Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin sun kashe ‘yan sanda biyu tare da yin garkuwa da wasu ma’aurata a jihar Anambra
  • Ma’auratan na a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama na Owerri, jihar Imo, lokacin da lamarin ya afku
  • Sai dai kakakin yan sandan jihar ya ce bai samu jawabi kan hakan ba tukuna

Anambra - Wasu tsagerun yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda biyu sannan suka yi garkuwa da wasu ma’aurata a jihar Anambra.

Jaridar Punch ta rahoto cewa al’amarin ya afku ne a yankin Okija da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.

An tattaro cewa ma’auratan na a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama na Owerri, jihar Imo, lokacin da maharan suka far masu.

'Yan bindiga sun sace ma'aurata a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama, sun kashe 'yan sanda dake raka su
'Yan bindiga sun sace ma'aurata a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama, sun kashe 'yan sanda dake raka su Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Zuwa yanzu ba a san ko su wanene suka sace su da kuma dalilin sace sun ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

Kakakin yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya ce bai riga ya samu jawabi kan lamarin ba.

Sai dai rahoton Daily Post ya kawo cewa wani babban jami’in dan sanda, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Jami’in ya yi bayanin cewa yan bindiga sun dauke ma’auratan a Ukpor, karamar hukumar Nnewi na jihar, a daren ranar Litinin.

Wani dan uwan ma'auratan ya tabbatar da lamarin

Wani dan uwan ma’auratan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an yi garkuwa da su a Okija a hanyarsu ta zuwa filin jirgi a Owerri.

Majiyar ta ce maharan sun kashe jami’an yan sanda biyu da ke tare da ma’auratan.

An tattaro cewa yan bindigar sun garkame mijin yayinda aka kwashi direban da ya jikkata zuwa wani asibiti.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

Ya ce:

“Sun sake su da misalin karfe 11:00 na dare. Daya daga cikin yan uwansu ya amsa kira daga daya daga cikinsu cewa a aiko direba ya zo ya kwashe su a Ukpor, inda suka ajiye su.
“Mun shiga rudani. A daren jiya na dawo Anambra. Na gode wa Allah suna nan a raye kuma sun dawo cikin al’ummarsu.”

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

A wani labarin, yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in tsaro yayin da suka kai farmaki garin Rigachukun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

A cewar wasu shaidu, an yi awon gaba da jami’in tsaron ne tare da wasu mazauna yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng