Cikakken jerin yankunan da uwar jam'iyyar APC ta baiwa kujeru a zaben shugabanninta
Gabanin taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), an baiwa yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya kujeran Shugaban jam'iyya.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan ganawar Gwamnonin jam'iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja don raba kujerun.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce duk kujerun da yankin Arewa ke rike da su yanzu za'a mayarwa yankin kudu.
Ranar 26 ga Maris aka dage zabe da taron gangamin.
Ga jerin yankuna da kujeran da aka basu:
Kudu maso kudu
(Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da Rivers )
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
2. Kakakin jam'iyya na kasa
3. Shugabar matan jam'iyya
4. Mataimakin ma'ajin jam'iyyar
5. Mataimakin sakataren nishadi
Kudu maso yamma
(Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun, da Oyo)
1. Sakataren Jam'iyya na kasa
2. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
3. Shugaban matasan jam'iyyar na kasa
4. Mataimakin shugaban Odita na kasa
Kudu maso gabas
(Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo )
1. Mataimakin shugaban jam'iyya (na kudu gaba daya)
2. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
3. Ma'ajin jam'iyya na kasa
4. Shugaban kula da nishadi na kasa
5. Mataimakin sakatren shirye-shirye na kasa
Arewa maso gabas
(Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe )
1. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
2. Odita na kasa
3. Mataimakin sakataren kudi na kasa
4. Mataimakiyar shugabar mata na kasa
Arewa maso tsakiya
(Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, da Plateau )
1. Shugaban jam'iyya
2. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
3. Mataimakin sakatare na kasa
4. Mataimakin mai ada shawara kan harkokin doka
5. Mataimakin Kakakin jam'iyya na kasa
Arewa maso yamma:
(Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara )
1. Mataimakin shugaban jam'iyya (na yankin)
2. Lauyan jam'iyya na kasa
3. Shugaban shirye-shirye na kasa
4. Sakataren kudi na kasa
5. Mataimakin shugaban matasa na kasa
Asali: Legit.ng