Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna
- Yan bindiga sun farmaki garin Rigachukun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a safiyar Laraba, 23 ga watan Fabrairu
- A yayin harin, yan bindigar sun sace jami'in tsaro da wasu mazauna yankin
- Maharan sun dauki tsawon lokaci suna harbi kan mai uwa da wabi ba tare da cikas ba
Kaduna - Yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in tsaro yayin da suka kai farmaki garin Rigachukun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewar wasu shaidu, an yi awon gaba da jami’in tsaron ne tare da wasu mazauna yankin.
Rahoton ya kawo cewa yan bindigar sun farmaki garin da ke kusa da Kasan Dam da misalin karfe 1:00am.
An tattaro cewa yan bindigar na ta harbi kan mai uwa da wabi inda suka ci karensu babu babbaka.
Wata matar aure da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce daya daga cikin wadanda aka sace abokin mijinta ne.
Ta ce:
“Ba mu iya yin bacci ba saboda karan harbi da ya dauki tsawon mintuna. Mutane hudu aka sace, ciki harda wani jami’in tsaro, wanda ke zama da mu a garin.”
Hakazalika, wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa a matsayin Zaid ya bayyana cewa yan bindigar sun raunata mutum daya wanda aka kwasa zuwa asibiti domin ya ga likita.
Ya yi bayanin cewa daga bisani an sako mata da yaron wanda aka raunata bayan an sace su.
Babu wani rahoto game da wannan lamari daga gwamnatin jihar ko rundunar yan sanda.
Kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran waya ba.
Tashin hankali: Sa'o'i 24 da kaurowarsu, 'yan haya sun sace yaran gida sun tsere
A wani labarin, wasu mata biyu sun yi garkuwa da yaran makwabtansu uku kasa da sa’o’i 24 bayan komawarsu sabon gidan da suke haya a yankin Ajuwon da ke jihar Ogun.
An tattaro cewa lamarin ya afku ne a unguwar Itsekiri da ke Ajuwon, jihar Ogun.
Wadanda ake zargin sun yi awon gaba da yaran ne a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng