Karin bayani: Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6
- Kotun babban birnin tarayya Abuja ta ba hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi damar ci gaba da tsare Abba Kyari
- Hakazalika, NDLEA ta samu damar ci gaba da bincikar sauran mutum shida da ke tare da Abba Kyari a tuhumar da ake masa
- Kotun ta ce ta ba NDLEA kwanaki 14, sannan ta ba da kofa su sake neman karin lokaci idan hakan ya taso a nan gaba
FCT, Borno - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar NDLEA na neman izinin ci gaba da tsare Abba Kyari da wasu mutum shida da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta bayar da umarnin a tsare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus na tsawon kwanaki 14 a cibiyar NDLEA da ke Abuja kafin a gudanar da bincike, inji rahoton The Nation.
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, ci gaba da tsare Abba Kyari da 'yan tawagarsa zai ba hukumar ta NDLEA damar ci gaba da bincike mai zurfi kan lamarinsa, kamar yadda lauyan NDLEA ya nema.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta ba da wannan umarni ne bayan ta saurari shugaban lauyoyin NDLEA, Joseph Sunday wanda ya nemi a ci gaba da ajiye mutanen.
Hakazalika, kotun ta ce hukumar na da ‘yancin sake neman karin wa’adin tsare wadanda ake zargin, bayan cikar wa’adin kwanaki 14.
Yadda aka kama abokan harkallar Kyari
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar (DFPRO), Olumuyiwa Adejob, a wata sanarwa da ya fitar kwanan nan, ya ce:
“Rahoton bincike da ke hannu ya nuna cewa an kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa guda biyu masu suna Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus, dukkansu maza, a filin jirgin saman Akanu Ibiam, Enugu, a ranar 19 ga watan Janairu.
“Kamen ya kai ga gano wani abu mai yawa na gari da ake zargin hodar Iblis ne daga ma’aikatan safarar guda biyu."
Hakazalika, sanarwar ta ce, rundunar Abba Kyari ta IRT ne ta gudanar da aikin kamen.
Adejobi ya ce daga bisani an mika wadanda ake zargin zuwa ga hukumar NDLEA a ranar 25 ga watan Janairu.
Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna
A wani labarin, wani dan sanda mai suna Sajan Adegoke Ogunsola ya mutu a gidan tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Jami'in ya bayyana cewa Ogunsola ya kasance ma'abocin zama a gidan tsohon gwamna Daniel, wanda aka fi sani da Kotun Asoludero, a garin Sagamu a karamar hukumar Sagamu ta jihar.
Asali: Legit.ng