Tashin hankali: Sa'o'i 24 da kaurowarsu, 'yan haya sun sace yaran gida sun tsere
- Wasu mata biyu sun tsere da wasu kananan yara uku a yankin Ajuwon da ke jihar Ogun
- Matan sun aiwatar da mugun nufin ne kasa da sa'o'i 24 bayan tarewarsu a gidan da suka yi haya
- Sun dai dauki yaran ne da nufin rakasu wani shago da ke makwabtaka da su, daga nan kuma sai ba a sake jin doriyarsu ba
Ogun - Wasu mata biyu sun yi garkuwa da yaran makwabtansu uku kasa da sa’o’i 24 bayan komawarsu sabon gidan da suke haya a yankin Ajuwon da ke jihar Ogun.
An tattaro cewa lamarin ya afku ne a unguwar Itsekiri da ke Ajuwon, jihar Ogun.
Wadanda ake zargin sun yi awon gaba da yaran ne a ranar Juma’a.
Wata majiya ta bayyana cewa matan wadanda ke a tsakanin shekaru 30 sun yi hayar daki daya ne a gidan inda suka tare ciki a ranar 17 ga watan Fabrairu, jaridar The Cable ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar wata majiya, matan sun yi ikirarin cewa su dalibai ne a wata makaranta da ke yankin Ikeja, jihar Lagas, kuma cewa za su shafe tsawon makonni uku a gidan, zuwa lokacin da za su kammala jarrabawarsu.
Sai dai kuma, majiyar ta ce ba su bayyana sunan makarantar ba.
Rahoton ya nuna cewa matan sun kasance masu faran-faran da mazauna gidan a cikin dan kankanin lokacin da suka yi a ciki.
A yammacin ranar Juma’a, sai matan suka nemi jan kafa tare da yaran domin siyan abu a wani shago da ke makwabtaka da su.
Sai dai kuma, bayan dan wani lokaci, sai aka fara neman sabbin yan hayan da yaran amma ko sama ko kasa ba a gansu ba.
An kai rahoton lamarin ofishin yan sandan Ajuwon.
Da take zantawa da jaridar The Cable, Grace, matar wani mutum mai suna Kingsley Peter, ta ce an kama mijinta kuma jami’an yan sanda sun ki sakinsa duk da cewar sun kama mai askin da ya hada wadanda ake zargin da mijinta.
Ana gudanar da bincike kan lamarin
Da aka tuntubi Abimbola Oyeyemi, kakakin yan sandan jihar Ogun, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce bai da labarin kama wani. Ya dai ce an gayyaci wasu a kan al’amarin.
Ya ce:
“Mun samu labarin lamarin. Ana kan bincike. Masu garkuwan sun yi hayan daki ne a wani gida. Kwanan nan suka tare a gidan kuma sauran makwabta basu san cewa suna da irin wannan shirin ba.”
Yan bindigar da suka sace kansila a Sokoto sun nemi a biya kudin fansa miliyan N60
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane tara ciki harda wani kansila mai ci a kauyen Yar Tsakuwa da ke karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto, sun nemi a biya naira miliyan 60 kudin fansa.
Daily Trust ta rahoto cewa wani mazaunin yankin, Nazifi Abdullahi, ya bayyana cewa yan bindigar sun kira yan uwan wadanda aka sace sannan sun nemi su hada kudin.
Asali: Legit.ng