An ji karar harbin bindiga, alkalin kotun daukaka kara ta sha da kyar, an nemi direbanta an rasa

An ji karar harbin bindiga, alkalin kotun daukaka kara ta sha da kyar, an nemi direbanta an rasa

  • Babbar alkalin kotun daukaka kara ta Owerri, Justice Rita Pemu ta sha da kyar bayan ta tsere wa masu garkuwa da mutane a ranar Lahadi
  • A takardar da sakataren kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA, reshen Owerri, Chinedu Agu ya sanya hannu, ya nuna yadda har yanzu babu wanda ya san inda direban ta yake
  • A cewarsa, lamarin ya auku ne akan titin Azia-Orsumoghu-Ihiala da misalin karfe 11 na safe yayin da ta gamu da miyagun mutanen wadanda suka tasa keyarta cikin daji

Jihar Imo - Babbar alkalin kotun daukaka kara ta Owerri, Justice Rita Pemu a ranar Alhamis ta tsallake rijiya da baya bayan ta gudu daga hannun wasu masu garkuwa da mutane.

A wata takarda wacce sakataren kungiyar lauyoyi ta kasa, reshen Owerri, Chinedu Agu, ya sanya hannu, ya ce har yanzu dai ba a ga direban ta ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wawure kudin kasa: Kotu ta tasa keyar tsohuwar minista da wasu mutane 2 zuwa gidan yari

An ji karar harbin bindiga, alkalin kotun daukaka kara ya sha da kyar, an nemi direbansa an rasa
Alkalin kotun daukaka kara ya sha da kyar, an nemi direbansa an rasa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cewarsa, al’amarin ya auku ne a kan titin Azia-Orsumoghu-Ihiala.

Da safe lamarin ya auku

Kamar yadda ya labarta:

“Jiya, ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairun 2022, an yi garkuwa da alkalin kotun daukaka kara yayin da take hanyarta ta zuwa Owerri daga Benin City, akan titin Azia-Orsumoghu-Ihiala da misalin karfe 11 na safe.
“Yayin da shugaban kungiyar lauyoyi, J.I. Ogamba da sakataren kungiyar, Chinedu Agu, suka kai mata ziyara yau da misalin karfe 5 na yamma, sun samu labari a ofis akan yadda masu garkuwa da mutanen suka zagaye abin hawan ta sannan suka bukaci ta fito ta durkusa musu tare da nuna mata bindiga a kan ta.
“Yayin da masu garkuwa da mutanen suka ga Justice Pemu sanye da wata riga mara tsada kuma cikin wata mota bas ba SUV dinta ba sun yi zaton ma’aikaciyar ta ce.”

Kara karanta wannan

Obasanjo: Abin Da Ƴan Boko Haram Suka Faɗa Min A Lokacin Da Muka Haɗu

Bayan sun tasa keyarta cikin dajin ne ta samu ta labe a wani wuri

Daily Trust ta ci gaba da bayyana yadda suka tasa keyar ta cikin duhun daji zasu kai wa shugaban su. Daga nan ta samu ta labe a wani wuri wanda daga bisani ta shiga garin Orlu har ta koma Owerri.

Ya ci gaba da cewa har lokacin da ya rubuta rahoton, ba a ga direbanta ba da kuma motarta ta wurin aiki.

Ya kara da cewa kullum cikin alawadai suke yi da garkuwa da mutane tare da rashin tsaron da ke jihar. Amma ya yi hamdala akan yadda Ubangiji ya tsare rayuwar Justice Rita Pemu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164