Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi
- Kungiyar ASUU ta yi martani ga gwamnatin tarayya da tace sam batasan kungiyar ta shiga yajin aiki ba
- Kungiyar ta kuma sake jaddada kokawarta kan yadda gwamnatin Buhari ke tafiyar da harkar ilimi a kasar
- ASUU ta ce ta fahimci gwamnati ta mayar da lakcarori bayi a kasar nan, don haka akwai gyara da ya kamata ta yi
Ibadan, jihar Oyo - Jaridar The Nation ta rahoto cewa, kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya da ke karkashinsa da daukar mambobinta tamkar bayi.
Kungiyar ta ce suna saurare ne kawai tare da aiwatar da abin da ta kira shawarwarin ruguza manufofin Asusun lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya sabanin yadda ‘yan Najeriya ke so.
Kungiyar ta kuma ce, munanan manufofin da aka tsara da kuma aiwatar da su a fannin Ilimi ya sanya gwamnati ta dauki malaman tamkar bayi.
ASUU ta yi barazanar yakar yadda gwamnati ke walagigi da lakcarorin kasar ta hanyar yin aiki don samar da ingantaccen yanayin aiki da ya hada da albashi da alawus-alawus tare da samun ingantaccen muhallin koyo ga dalibai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kungiyar na Jami’ar Ibadan (UI), Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu a birnin Ibadan ta jihar Oyo.
Ya fadi haka ne a martaninsa kan zargin da ministan ilimi Adamu Adamu ya yi na cewa yana kokarin magance matsalolin da ke ci gaba da tabarbarewa tsakanin ASUU da gwamnati lokacin da ya ji cewa kungiyar ta ayyana shiga yajin aiki.
Akinwole ya ce Gwamnatin Tarayya da masu ruwa da tsaki a ma’aikatar ilimi ta kasar sun nuna ko in kula da kuma dabi’un da ba su dace ba a kan batutuwan da suka shafi ‘yan Najeriya.
Shugaban ASUU ya ce ba gaskiya ba ne ace wani dan Najeriya ya yi ikirarin rashin sani game da jerin gargadin da kungiyar ta yi a cikin wata daya da ya gabata kafin ta yanke shawarar tsundumawa yajin aiki.
Duk laifin gwamnati ne, lakcarori na mutuwa, wasu na barin Najeriya
Ya kuma bayyana cewa, sakamakon gazawar da gwamnati ta yi na daukar karin ma’aikatan jami’o’i, ya sa ‘yan kungiyar ASUU da dama sun mutu yayin da wasu kuma suka bar kasar nan zuwa kasashen ketare.
Jaridar Vanguard ta rahoto Akinwole yana bayyana yadda kungiyar ta sha fama da yarjejeniya tsakanin ta da gwamnati tun 2009; tsawon shekaru 13 kenan.
The Nation ta rahoto shi yana cewa:
“Gwamnatin Tarayya ba ta da gaskiya. Abin bakin ciki ne. Gwamnati ba abar yarda bace yanzu kam. Mun yi shekara 13 muna karbar albashi ba kari, ya ma zama abin kunya mu nuna wa wani takardar biyan mu.
“Idan aka kwatanta da aikin da muke yi, mun sadaukar da kai ga Najeriya ko da kuwa za mu cutar da lafiyarmu. Wannan tuni ya riga ya dakushe kwarin gwiwar mutanenmu.
"Ya kamata gwamnatin tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka sake tattaunawa akanta, ta aiwatar da ita, ta fitar da UTAS, ta biya alawus din karatun da ba a biya ba, sannan ta kara kashe kudade wajen farfado da jami'o'i."
Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata
A wani labarin, Adamu Adamu, ministan ilimi, ya ce matakin yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na wata daya "abin mamaki ne".
Ya ce ba laifin gwamnatin tarayya ba ne idan har ba a cimma matsaya ba bayan tattaunawa da dama tsakanin bangarorin biyu, TheCable ta ruwaito.
Ministan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Asali: Legit.ng