Tinubu ya san matsalolin Najeriya kamar tafi hannunsa, Gwamnan Legas
- Yan siyasan jihar Legas sun bayyana niyyar hada karfi da karfe wajen tabbatar da Tinubu ya dane kujerar shugaban kasa
- Gwamna Legas ya yi kira ga yan majalisan dokokin jihar sun ajiye banbancin siyasarsu gefe guda su yiwa Tinubu aiki
- Tsohon Gwamnan Legas Tinubu ya bayyana niyyar takara a zaben kujeran shugaban kasa a 2023
Ikeja, jihar Legas - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayyana cewa Jagoran APC Asiwaju Bola Tinubu ya san matsalolin Najeriya kamar tafin hannunsa.
Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a jihar Legas yayin taron hadin kan yan majalisa dokoki da yan majalisar zartaswar jihar, rahoton DailyTrust.
Ya ce Tinubu ya sadaukar da kansa wa al'ummar Legas lokacin mulkinsa matsayin Gwamna da kuma Najeriya gaba daya.
Yace:
"Gaskiya lokaci yayi da zamu biyashi da goyon bayanmu. Ko shakka babu shine wanda ya cancanci aikin. Ya san matsalolin kasar nan kamar tafin hannunsa kuma yana da asirin gyara ta."
"Saboda haka, lokaci yayi da za'a tura dan Legas birnin tarayya."
"Shiyasa nike kira gareku mu tabbatar da cewa mun yi duk mai yiwuwa don taimakawa Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban kasa."
Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce yanzu ne lokacin da arewa za ta marawa kudirin takarar shugabancin kasa na babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya.
A wata hira da jaridar Daily Trust, Shettima ya ce lallai lokaci ne na sakawa Tinubu wanda ya tabbatar da ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma dadaddiyar burinsa.
Ya ce da taimakon jigon na APC ne Buhari ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben na 2015.
Asali: Legit.ng