Yanzu: Buhari, Jonathan da sauran manyan 'yan Najeriya sun hallarci wurin bikin zagayowar ranar haihuwar Anyim
- Yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da sauran masu fadi a ji a Najeriya suna wurin shagalin zagayowar ranar haihuwar Anyim Pius Anyim
- Anyim tsohon shugaban majalisar dattawa ne, kuma a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu yake cika shekaru 61, hakan yasa aka shirya liyafa ta gani da fadi a International Conference Centre, Abuja
- Buhari ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda ya isa da misalin karfe 11:07 na safe tare da sauran hadimai da ma’aikata wadanda suka raka shi
Abuja - Yanzu haka kusoshin Najeriya har da Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan sun taru a International Conference Centre da ke Abuja don shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban majalisar wakilai, Anyim Pius Anyim, wanda ya cika shekaru 61 a ranar Asabar, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban Kasa ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha wanda ya isa wurin da misalin karfe 11:07 na safe inda hadimai da sauran mutane suka masa rakiya.
Dr. Jonathan shi ne shugaban taron kuma yayin jawabin bude taron ya yaba wa Ayim akan dabi’unsa na kwarai a lokacin yana shugaban majalisar dattawa daga bisani kuma ya zama sakataren gwamnati tarayya, inda ya jajirce wurin yi wa kasa aiki.
Jawabin Jonathan ya yi kama da yi wa Anyim kamfen
Vanguard ta bayyana yadda jawabin Jonathan ya yi kama da nuna goyon baya ga kudirin Anyim na tsayawa takarar shugabancin kasa, inda Jonathan ya fadi ayyukan kwarai da yayi a mukaman da ya rike a baya.
Jonathan ya kara da cewa Anyim zai yi fiye da haka idan aka bashi dama.
Sauran wadanda suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara da tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da sauran su.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng