Kano: Ya Jefa Yaro Cikin Rijiya Bayan Yin Rikici Da Mahaifin Yaron, Kotu Ta Ce a Tsare Shi a Gidan Gyaran Hali
- Wata kotun Majistare a Kano ta bada umurnin a ajiye wani mutum da ake zargi da jefa yaro cikin rijiya masauki a gidan yari
- Mai gabatar da kara ta ce wanda ake zargin Abubakar Aminu ya jefa yaro, Abdulmalik Suleiman a rijiya ne bayan ya yi rikici da mahaifinsa
- Amma wanda ake zargin ya musanta aikata laifin don haka alkali ya ce a ajiye shi a gidan gyaran hali ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar
Kano - Alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Juma'a, ya bada umurnin a tare wani mutum mai shekaru 33, Abubakar Aminu, a gidan gyaran hali kan zarginsa da jefa yaro dan shekara hudu, Abdulmalik Suleiman cikin rijiya.
An tuhumar wanda aka yi karar, mazaunin Rijiyar Lemo Quaters a Kano da laifin yunkurin aikata kisa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Asali: UGC
Yadda abin ya faru
Mai gabatar da karar, Asma'u Ado, ta sanar da kotu cewa wani Aminu Suleiman mazaunin Bachirawa Quaters, a Kano ne ya kai rahoton afkuwar lamarin a ofishin yan sanda na Rijiyar Lemo a Kano a ranar 14 ga watan Oktoban 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ado ta ce yaron dan shekara hudu dan wanda ya yi korafin ne.
Ado ya yi ikirarin cewa a ranar, misalin karfe 2 na rana, wanda aka yi karar ya samu rashin jituwa da wanda ya yi karar, hakan yasa wanda aka yi karar ya jefa yaron cikin rijiya a Bachirawa Quaters da gangan.
Ya ce an ceto yaron sannan aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin a yi masa magani, rahoton Vanguard.
Mai gabatar da karar ya ce laifin ya ci karo da sashi na 229 na dokar Penal Code.

Kara karanta wannan
Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina
Wanda ake zargi ya musanta laifin
Wanda aka yi karar ya musanta aikata laifin da ake tuhumansa.
Babban alkalin kotun, Mustapha Sa'ad-Datti, ya dage cigaba da sauraron karar har sai ranar 21 ga watan Fabrairu kamar yadda NAN ta rahoto.
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng