Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga
- Sabon kwamishinan yan sanda da aka tura jihar Katsina ya shawarci yan bindiga su gaggauta aje makamansu kuma su tuba
- CP Idrisu Dauda Dabban, yace dakarun yan sanda za su yi aiki tukuru da taimakon Allah wajen kawo karshen ta'addanci a jihar
- Ya roki al'ummar jihar Katsina sun taimaka musu da bayanan sirri domin hakan ne kaɗai zai sa su samu nasara
Katsina - Sabon kwamishinan yan sanda da aka tura Katsina, CP Idrisu Dauda Dabban, ya shawarci yan ta'adda su tuba su miƙa wuya daga ayyukan sheɗanci kafin dakarun yan sanda su iso gare su.
Vanguard ta rahoto cewa sabon kwamishinan ya yaba da namijin kokarin wanda ya gaji kujerar a hannunsa, AIG Sanusi Buba.
Punch ta rahoto A jawabinsa ya ce:
"Na zo nan ne na ɗora daga dai-dai inda wanda na gada, AIG Sanusi Buba, ya tsaya domin ya yi aiki tukuru. Mun san babban matsalar da hukumar nan ke fama da ita."
"Ayyukan ta'addancin yan bindiga babban abin takaici ne, amma za mu yi bakin kokarin mu kuma da taimakon Allah zamu samu nasara."
"Duk wani abu da akace laifi ne baya haifar da sakamako mai kyau. Ya kamata yan bindiga su watsar da ta'addanci su miƙa wuya ko kuma mu rutsa su da taimakon Allah."
Shin wane mataki sabon CP ɗin zai bi?
Kwamishinan ya jaddada bukatar haɗin kai da goyon bayan Katsinawa domin cimma nasarar magance ayyukan yan bindiga da sauran manyan laifuka.
"Ina rokon goyon bayan mutanen jihar nan baki ɗaya, ku taimaka mana da sahihan bayanai domin mu samu nasara. Ba tare da bayanan sirri daga gare ku ba, ba zamu iya cimma yan ta'adda ba."
"Saboda haka muna bukatar haɗin kan ku da goyon baya domin kawo karshen yan bindiga a faɗin jihar nan."
A wani labarin na daban kuma An kama wani Mutumi da zargin tafka wa diyarsa mari har ta mutu a jihar Jigawa
Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan kimanin shekara 40 bisa zargin bugun ɗiyarsa Salima Hannafi, har lahira a jihar Jigawa.
Bayanai sun nuna cewa magidancin, Hannafi Yakubu, ya tafka wa yarinyar mari ne, kuma Allah ya karbi rayuwarta a karamar hukumar Babura.
Asali: Legit.ng