Da dumi-dumi: Najeriya da wasu kasashen Afrika 5 za su fara kera riga-kafin Korona, WHO
- Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amincewa Najeriya ta fara kera alluran riga-kafin Korona a cikin gida
- Hakazalika, hukumar ta kuma amincewa kasashen Afrika guda biyar su fara wannan hidima, kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Hukumar ta ce za ta samar da abubuwan da ake bukata ta fasaha ga kasashen domin fara wannan aiki na kera riga-kafin
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amincewa Najeriya da wasu kasashen Afrika 5 domin su fara kera allurar riga-kafin Korona ta mRNA, inji rahoton Punch.
WHO ta amince da kasashen Masar, Kenya, Senegal, frica ta Kudu, da Tunisia tare da Najeriya, inda za a samar musu da cikakkiyar fasahar da suke bukata domin samar da riga-kafin.
Darakta Janar na WHO, Dr Tedros Ghebreyesus, ya sanar da kasashen shida na farko da za su sami fasahar ne a taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka yi a Brussels ranar Juma'a.
Sanarwar an yi ta ne a taron da Majalisar Turai, Faransa, Afrika ta Kudu da WHO suka shirya, an kuma sanar da hakan ne a gaban shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, shugaba Ramaphosana, shugaban Majalisar Turai Charles Michel, da dai sauran jiga-jigai.
Wani bangare na sanarwar da SaharaReporters ta rahoto ya ce:
“Masar, Kenya, Najeriya, Senegal, Afirka ta Kudu da Tunisia duk sun mika bukata kuma an zabe su a matsayin wadanda za su karba.
"An kafa cibiyar fasahar mRNA ta duniya a 2021 don tallafawa masana'antu a kasashe masu karanci da matsakaicin tattalin arziki don samar da nasu rigakafin, tabbatar da cewa suna da dukkan hanyoyin da suka dace da kuma sanin yadda ake kera allurar mRNA akan tsarin kasa da kasa."
WHO ta ce, ba kasashen damar samar da alluran riga-kafin zai cike gibin yawan bukatuwa ga allurar riga-kafin Korona.
Har yanzu dai kasashen duniya na ci gaba da fuskantar kalubalen annobar Korona, hakazalika, akan samu karancin shigo da alluran riga-kafi, musamman a kasashen Afrika.
Gwamnatin Buhari ta fara bin coci don yiwa masu bautar ranar Lahadi riga-kafin Korona
Gwamnatin tarayya a ranar Talata 14 ga watan Satumba ta sanar da shirinta na daukar allurar riga-kafin Korona zuwa cibiyoyin bauta ta Kiristoci, Punch ta ruwaito.
Babban Darakta na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan ne yayin wayar da kan shugabannin Kiristoci kan kashi na biyu na riga-kafin Korona a babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce:
“Mai martaba, Shugaban CAN, fitattun shugabannin Kirista, mata da maza, ina mai farin cikin sanar da ku cewa daga wannan mataki na 2 na riga-kafin Korona, mun gabatar da allurar riga-kafin ranar Lahadi."
Asali: Legit.ng