Yadda matar aure ta kashe mijinta, Bello, da tafasasshen ruwa a Ogun

Yadda matar aure ta kashe mijinta, Bello, da tafasasshen ruwa a Ogun

  • Ana zargin Ramota Soliu da halaka mijin ta, Bello Saliu ta hanyar watsa masa tafasashshen ruwa a anguwar Fulani da ke yankin Iyana Ilewo a karamar hukumar Abeokuta ta arewa da ke jihar
  • An samu bayanai akan yadda matar mai yara biyu da marigayin suka kwashe shekaru 6 suna soyayya kafin wannan mummunan lamarin ya auku
  • Wata majiya ta bayyana yadda tun ranar Juma’ar da ta gabata marigayin ya gayyaci ‘yan uwansa don su ba matar sa hakuri saboda a samu zaman lafiya tsakanin su

Ogun - Wata Ramota Soliu ta halaka mijin ta, Bello Soliu ta hanyar watsa masa tafasashshen ruwa a anguwar Fulani da ke yankin Iyana Ilewo da ke karamar hukumar Abeokuta ta arewa da ke jihar.

Manema labarai sun tattaro bayanai akan yadda ta watsa wa Bello ruwan zafin wanda ya yi ajalin sa, Nigerian Tribune ta ruwaio.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Yadda matar aure ta kashe mijinta da tafasasshen ruwa a Ogun
Matar aure ta antayawa mijinta tafasasshen ruwa ta tsere. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Matar mai yara biyu ta kwashe shekaru 6 suna soyayya da mijin ta kafin wannan mummunan lamarin ya ratso.

The Sun ta ruwaito yadda mamacin ya gayyaci ‘yan uwan sa don su ba matar sa hakuri akan laifukan da ya yi mata.

Dama ta saba cutar da mijin nata

Matar ta saba hana shi da wani almajiri da ke zama da su abinci.

Daya daga cikin ‘yan uwan mammacin, Usman Soliu, ya ce wacce ake zargin ta tashi da safiyar Asabar inda ta tafasa ruwa ta watsa wa mijin ta.

A cewarsa:

“Dan uwana ya dade yana korafi akan matar sa Ramota. Ta saba barin shi da almajirin da ke zama da su da yunwa. Duk don neman zaman lafiya, Bello ya gayyace mu don mu ba ta hakuri.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

“Bata ce komai ba. Sai da safiyar Asabar ta falka ta tafasa ruwan zafi. Mutane sun zaci Amala ko Ogi za ta dafa don ta kai awa daya tana dafa wa. Yana tsaka da bacci ta antaya masa ruwan.
“An yi gaggawar wucewa da shi asibiti lokacin jikin sa duk ya sulbe. A ranar Talata da yamma ya rasu.”

Yanzu haka ana ta neman matar

A cewar dan uwan mamacin, Aliu Soliu, an dade da birne mamacin. Kuma yanzu haka ana ta neman wacce ta yi aika-aikar.

Jami’in hulda da jama’an ‘yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kamar yadda ya ce:

“Na ji labarin aukuwar lamarin a gidan rediyo. Amma ban tabbatar idan sun kai korafi ofishin ‘yan sanda ba."

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kara karanta wannan

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164