Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa bada kwangilar bogi a jihar Bauchi

Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa bada kwangilar bogi a jihar Bauchi

  • Wani jami'in gwamnatin jihar Bauchi, Baba Suleiman Darazo, ya gamu da fushin alkali
  • Mai shari’a Muazu Abubakar na babbar kotun jihar Bauchi ya yankewa Darazo hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda cin amanar aiki da zamba
  • Darazo dai ya yi amfani da takardar hukumar shari'a ta jihar wajen bayar da kwangilar bogi na kawo kwamfutoci 5,000 ga wani kamfani

Bauchi - Mai shari’a Muazu Abubakar na babbar kotun jihar Bauchi, ya zartar da hukunci a kan wani Baba Suleiman Darazo, babban direba a hukumar shari’a ta jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar AUPCTRE reshen Bauchi.

A ranar Talata ne Alkali Abubakar ya yankewa Darazo hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda cin amanar aiki da zamba.

Kara karanta wannan

Harkar kwaya: Abba Kyari zai iya karasa rayuwarsa ta Duniya a kurkuku a dokar NDLEA

Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa ba kwangilar bogi a jihar Bauchi
Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa ba kwangilar bogi a jihar Bauchi Hoto: Thisday
Asali: UGC

Yadda abun ya faru

Channels TV ta rahoto cewa Darazo dai ya samo takardu biyu daga ofishin sannan ya yi amfani da su wajen bayar da kwangila ga wani kamfani domin su yo wa kungiyar AUPCTRE odar kwamfutoci guda 5,000.

Mai laifin ya nunawa kamfanin kamar hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Bauchi ce ta bayar da kwangilar.

Ya kuma kirkiri takardun umarnin biyan kudi na bogi ga kamfanin domin tabbatar da ya rufe badakalarsa.

An yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Sai dai an ba shi zabin biyan tarar N100, 000.

Kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da N430, 000 da ya karba a matsayin kudin dillanci daga hannun manajan kamfanin da ya damfara, rahoton EFCC.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake da kura-kurai

A wani labari na daban, hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC), a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa rahoton binciken da rundunar yan sandan Najeriya ta gabatar mata kan jami’inta, Abba Kyari, yana cike da kura-kurai da dama.

Hukumar wacce tun farko ta umurci rundunar da ta gudanar da sabon bincike tare da wani kwamiti na daban kan babban jami’in, sannan a gabatar da wani rahoto cikin makonni biyu, ta riki cewa dole a gabatar da sabon rahoto a tsakanin lokacin da ta bayar.

Ikechukwu Ani, kakakin hukumar, a wata hira da yayi da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, ya yi bayanin cewa kwamishinonin, karkashin jagorancin Musiliu Smith, Sufeto janar na yan sanda mai ritaya za su dauki sabon hukunci idan kura-kuran suka kara bayyana a sabon rahoton.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng