Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi
- Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin kwamishinan ‘yan sandan nan da aka dakatar, Abba Kyari ya fadi wasu bayanai yayin da hukumar NDLEA ta yi masa tambayoyi
- Majiya a NDLEA ta ce mganarsa za ta kai ga ci gaba da gudanar da bincike, lamarin da ya sa hukumar ta garzaya kotu domin ba ta damar tsare Kyari da sauran mutanensa hudu
- Rundunar ‘yan sanda a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta kama Kyari da wasu mutane hudu tare da mika su ga NDLEA bayan zarginsu da hannu a safarar miyagun kwayoyi
FCT, Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar tare da wasu 'yan tawagarsa mutane hudu na iya ci gaba da zama a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).
A cewar jaridar, hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta sanar da kotun aniyar ta na tsare wadanda ake zargin sama da awanni 48 da aka kayyade.
Da take zantawa da wata majiya mai tushe a hukumar, Punch ta bayyana cewa Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga kara bincike don haka hukumar ta NDLEA ba za ta iya gurfanar da shi a gaban kuliya ba.
An kuma bayyana cewa tuni hukumar ta NDLEA ta fara gudanar da bincike kan hodar iblis da babban jami’in ‘yan sandan ya nemi kulla harkallarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ruwaito daga majiyar tana cewa:
“Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga karin bincike. Har ila yau, hukumar ta NDLEA na gudanar da binciken kwakwaf kan wata hodar iblis da Kyari ya kwato tun bayan da ya yi ikirarin cewa a cikin wani faifan bidiyo ya maye gurbin hodar iblis din da tabar wiwi.
“Don haka hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda muka sanar da kotu aniyar mu na kara yi masa tambayoyi da kuma tabbatar da wasu daga cikin abubuwan da ya ce ya yi.”
Idan baku manta ba, rahotannin baya na Legit.ng Hausa sun bayyana cewa, ‘yan sanda sun kama Kyari a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu bisa zarginsa da alaka da miyagun kwayoyi tare da mika shi ga hukumar NDLEA da wasu mutane hudu.
Aiki da cikawa: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama shugaban tawagar hukumar leken asiri ta IRT, DCP Abba Kyari da aka dakatar.
Jaridar Punch ta tattaro cewa, an kama shi ne tare da wasu mutane hudu ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.
An kama Kyari ne sa’o’i kadan bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana cewa tana neman sa bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng