Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia
- Kungiyoyin arewa na CNG da AYCF sun yi watsi da harin da wasu yan bindiga suka kai kasuwar shanu da ke jihar Abia, inda suka kashe wasu yan arewa
- Hakazalika sun ce ya zama dole gwamnatin Abia ta gaggauta kamo wadanda suka kai harin wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka takwas
- Maharan sun kai farmakin ne a daren ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu
Gamayyar kungiyoyin arewa (CNG) da na matasan arewa (AYCF) sun yi Allah wadai da harin da aka kai kan yan arewa a kasuwar shanu da ke jihar Abia wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka, sun ce ba za a lamunci hakan ba.
Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu da ke garin Omumauzor, karamar hukumar Ukwa ta yamma a jihar Abia a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, da misalin 11:35 na dare, inda suka kashe mutane takwas.
Yayin da suke martani ga harin a sanarwa daban-daban, kungiyoyin sun yi watsi da lamarin sannan sun yi kira ga gwamnatin jihar Abia da ta hukunta wadanda suka aikata ta’asar, Daily Trust ta rahoto.
Kakakin kungiyar CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ce ya zama dole gwamnatin jihar ta gaggauta hukunta masu laifin sannan ya yi gargadin cewa arewa ba za ta kuma yarda da hare-hare mara tushe kan mutanenta da ke kudu maso gabas ko sauran yankin kasar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Suleiman ya ce:
“Mun yi nazarin lamuran a tsanaki kuma cikin lura da kamun kai, har ta kai mun lamunci wasu ayyuka na rashin tunani kuma wanda ba za a yarda da su ba da ake yiwa yan arewa musamman a kudu maso gabas.
“Tura ta kai bango a kan harin baya-bayan nan da aka kai a Abia kuma rashin daukar mataki ba zai zama mafita ba a wannan yanayi na kai hare-hare da kisan yan arewa a yankuna daban-daban na kudu maso gabas.”
Vanguard ta nakalto shugaban kungiyar matasan arewa ta AYCF, Alhaji Yerima Shettima yana cewa:
"A matsayinmu na kungiya, har yanzu muna cikin damuwa dangane da kisan yan arewa mazauna Abia, wadanda ke gudanar da kasuwancinsu na neman halal. Haka kuma zuciyarmu ta tabu sosai da rahoton sauran da suka jikkata kuma suke asibiti a yanzu."
Yayin da yake watsi da harin kan bayin Allah daga arewa wadanda ke neman na kai, ya yaba da matakin gaggawa da hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Abia suka dauka na bin sahun wadanda suka aikata kisan da kuma kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Ya bukaci gwamnatin jihar Abia da ta cika alkawarinta na hukunta wadanda suka aikata kisan a kokarin kawo hadin kai da daidaita kasa.
'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama
A baya mun kawo cewa 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a yayin wani farmaki da suka kai sabuwar kasuwar shanu ta Abia da ke Omumauzor, karamar hukumar Ukwa West da ke jihar Abia.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun kai farmakin ne a daren ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu.
An tattaro cewa harin tsakar daren ya sanya mazauna kauyen cikin halin firgici da tsoro.
Asali: Legit.ng