Karfin hali: An yi cacar baki tsakanin mai Shari'a da Nnamdi Kanu kan tufafinsa
- Kotun babban birnin tarayya ta nemi dalilin da yasa SSS suka ci gaba da kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya kala daya
- A rahoton da muka samo, wakilin SSS ya yi bayani, inda ya bayyana yadda ake kawo wa Kanu kayan da basu dace ba
- Nnamdi Kanu dai ya ci gaba da nacewa kan dole sai dai ya sanya wata kalar riga mai dauke da hoton kan zaki
FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta SSS, a ranar Laraba, ta shaidawa babbar kotun tarayya dake Abuja cewa, Nnamdi Kanu, shugaban IPOB, ba zai yiwu ya ci gaba da sanya tufafi masu dauke da alamar zaki ba.
Ana zargin Kanu da laifuffuka daban-daban da suka hada da na cin amanar kasa da ta’addanci, laifukan da ake zargin ya aikata a kacaniyar aware don kafa kasar Biafra, Premium Times ta rahoto.
A ci gaba da shari’ar a ranar Laraba, babban lauyan Kanu, Mike Ozekhome, ya ja hankalin alkali mai shari’a, Binta Nyako kan irin matsalolin da suke fuskanta a kokarin kai sabbin tufafi ga shugaban kungiyar ta IPOB a tsare a Abuja.
Misis Nyako dai ta umarci hukumar SSS da ta baiwa Kanu damar sauya tufafi daga rigar Fendi da ya saba sanyawa yake zuwa gaban kotu.
Da yake mayar da martani kan korafin Mista Ozekhome, alkalin ya bukaci Daraktan kula da shari’a na SSS da ba a bayyana sunansa ba da ya yi bayani kan lamarin.
A jawabinsa, ya shaidawa kotu cewa:
"Mai Shari'a, tufafin da aka kawo wa wanda ake kara akwai hoton kan zaki a jiki, kuma wanda ake kara (Mr Kanu) ba zai yiwu ya sanya tufafi da kan zaki ba."
Yayi karin bayani da cewa, “tufafi da kan zaki ya saba wa ka’idojin aiki” na SSS.
Sai dai Kanu ya dage kan sa tufafin kabilar Ibo da ke dauke da alamar zaki, rigar da ‘yan kungiyar IPOB ke sanyawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Cacar bakin Kanu da mai shari'a
Kafin tambayar wakilin na SSS, mai shari’a Nyako ta yi cacar baki da Kanu kan batun tufafinsa, inda tace bata son ganin kayan da yake zuwa dashi kotu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Da ta tambaye shi dalilin sanya irin tufafin, Kanu ya amsa da cewa:
"Ina so in sa tufafin mutanena wanda shine 'Isi-Agu'."
Mai shari'a ta ce masa:
"A'a, ba za ka sa ba.'
Kanu ya amsa da cewa:
"Amma na gaza fahimtar dalilin da ya sa ba zan saka ba."
Daga nan ne mai shari'a ta nemi bahasi daga wakilin SSS.
Idan baku manta ba, ana tuhumar shugaban kungiyar ta IPOB ne bisa wasu tuhume-tuhume 15 da aka gyara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya
A wani labarin, Mai shari'a ta babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bari Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan awaren IPOB da ya sauya kayayyakinsa.
A baya, Nyako ta umurci DSS da ta bari shugaban na IPOB ya dunga yin wanka a duk lokacin da yake son canja tufafinsa, ya ci abinci yadda ya kamata da kuma gudanar da addininsa.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa a zaman kotu na ranar Talata, 18 ga watan Janairu, Mike Ozekhome, lauyan Kanu, ya yi korafin cewa har yanzu wanda yake karewa baya samun kula mai kyau a hannun DSS.
Asali: Legit.ng