Yar’adua: Mahaifyar Ɗan Takarar Gwamna a Katsina Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Yar’adua: Mahaifyar Ɗan Takarar Gwamna a Katsina Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa Hajiya Hurera Sa'id, mahaifiyar tsohon dan takarar gwamna a Jihar Katsina, Sanata Abubakar Sadiq rasuwa
  • Hajiya Hurera ta rasu ne a ranar Talata a garin Yar'adua da ke birnin Katsina bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Manyan mutane da suka halarci jana'izarta sun hada da Gwamna Aminu Bello Masari, Alhaji Dahiru Mangal da sauransu

Jihar Katsina - Tsohon sanata mai wakiltan Katsina ta Tsakiya, Abubakar Sadiq Yar'adua, ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Hurera Sa'id.

Hajiya, wacce aka fi sani da Goggo, ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, Daily Trust ta ruwaito.

Ta rasu tana da shekaru 86 a duniya.

Yar’adua: Mahaifyar Ɗan Takarar Gwamna a Katsina Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
Mahaifyar Ɗan Takarar Gwamna a Katsina, Yar'adua, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An birne ta a makabartar Yammawa bayan an mata salla misalin karfe 5 na yamma a gidanta da ke Yar'adua a birnin Katsina.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda suka hallarci jana'izar Hajiya Hurera

Cikin manyan mutanen da suka hallarci jana'izarta akwai Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Mataimakinsa, Mannir Yakubu, babban dan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal.

Saura sun hada da Babban Direktan Federal Mortgage Bank, Ahmed Musa Dangiwa; Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Dr Mustapha Inuwa; Kwamishinan Wassani da Walwala, Alhaji Sani Danlami da takwararsa na filaye, Alhaji Usman Nadada da sauransu.

Rahotn na Daily Trust ta bayyana cewa Hajiya Goggo ta bar yara guda bakwai da jikoki masu yawa

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164