Manyan taƙaddama 5 da suka baibaye jarumin dan sanda Abba Kyari tun farko
- Mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari, ya fara shiga zargi ne tun shekarar da ta gabata
- Fitaccen ɗan damfaran nan na Intanet, Hushpuppi, shi ne ya fara saka gwarzon ɗan sandan cikin lamarin damfara a Amurka
- Mun tattara muku wasu manyan lamurra 5 da suka faru da shugaban tawagar yan sandan IRT tun bayan fara tuhumarsa a 2021
Abuja - Mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari, ya shiga cikin batutuwa da dama a kwanakin baya bisa wasu dalilai, kamar yadda daily trust ta rahoto.
Ɗan sandan da aka dakatar, wanda ya shahara a faɗin kasa saboda jarumtarsa, an alaƙanta shi da wasu laifuka da dama tun shekarar da ta gabata.
Mun tattaro muku wasu daga cikin taƙaddamar da aka yi game da ɗan sandan tun farko, ga su kamar haka:
1. A ranar 29 ga watan Yuli, shahararren ɗan damfaran nan na Intanet, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, wanda ke fama da tuhumar damfara a Amurka ya saka sunan Abba Kyari cikin masu hannu a damfarar wani mutumi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. A ranar ɗaya ga watan Augusta, 2021, hukumar jin daɗin yan sanda ta kasa (PSC) ta dakatar da mataimakin kwamishina kuma shugaban tawagar yan sandan IRT, domin martani kan tuhumar da ake masa.
3. A ranar 3 ga watan Agusta, 2021, Abba Kyari ya saki bayani a shafinsa na Facebook, inda yake bayyana alaƙarsa da Hushpuppi ta hanyar Telansa, wanda ɗan damfaran ya tura wa N300,000.
Daga baya Kyari ya yi wa rubutunsa kwaskwarima, inda ya sake bayani kan wata alaƙar kuɗi da ta haɗa shi da Hushpuppi.
Amma daga ƙarshe ya goge baki ɗaya bayanin da ya yi, wanda da farko ya yi ikirarin cewa sun ƙulla alaƙa da Hushpuppi ne ta hanyar Telansa.
4. Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ayyana neman Kyari ruwa a jallo bisa zargin hannu a shigo da muggan kwayoyi.
Hukumar ta kuma saki bidiyo da ake zargin Abba Kyari ne tare da wani mutumi suna tattauna batu kan Hodar Ibilis, duk haka ta faru ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022.
5. A wannan rana, Sa'o'i kaɗan bayan NDLEA ta ayyana neman Kyari ruwa a jallo, rundunar yan sanda ta ƙasa ta yi ram da shi tare da wasu mutane.
A wani labarin na daban kuma mun binciko muku Jerin abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku sani ba game da DCP Abba Kyari
A ranar Litinin, yan sanda suka kama DCP Abba Kyari, kuma suka miƙa shi hannun NDLEA bisa zargin safaran muggan kwayoyi.
Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku san su ba game da gwarzon ɗan sandan.
Asali: Legit.ng