Harkar kwayoyi: Abin da ya dace IGP ya yi wa Kyari ba tare da bata lokaci ba - Lauya

Harkar kwayoyi: Abin da ya dace IGP ya yi wa Kyari ba tare da bata lokaci ba - Lauya

  • Lauya ya bada shawarar cewa IGP Usman Alkali Baba ya bada umarni a damke DCP Abba Kyari
  • Pelumi Olajengbesi ya ce kai Abba Kyari gaban hukumar NDLEA zai nuna za a bar gaskiya tayi aiki
  • Olajengbesi mai kokarin kare hakkin al’umma ya ce bai dace ayi wata rufa-rufa a wannan lamarin ba

FCT, Abuja - Wani lauya mai kare hakkin al’umma da yake aiki a garin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya tofa albarkacin bakinsa a kan tirka-tirkar Abba Kyari.

Pelumi Olajengbesi ya yi kira ga Sufetan ‘Yan Sanda na kasa, Usman Alkali Baba, ya mika tsohon shugaban dakarun IRT, Abba Kyari ga hukumar NDLEA.

Punch ta ce Olajengbesi ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar a safiyar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022 bayan ya ji ana neman DCP Kyari.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NDLEA ta cafke Mutumin Indiya da aka samu da kwalaben codeine 134,000

A cewar Lauyan, ya kamata IGP Usman Alkali Baba ya sa a mikawa NDLEA wanda ta ke nema.

Jaridar ta rahoto wannan lauya mai kare hakkin Bil Adama yana cewa dole ayi wannan a gaban Duniya, idan har ana so a tabbatar da gaskiyar ‘yan sanda.

Abba Kyari
DCP Abba Kyari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dole ne Sufetan ‘Yan Sanda na kasa ya yi gaggawar bada umarni a cafke Abba Kyari, a kuma damka shi ga NDLEA.”
“Ayi wannan a taron manema labarai idan har da gaske ‘yan sanda ba su kokarin kare bara-gurbin da ke cikinsu.”
“Dole IGP ya nuna cewa ba ya goyon bayan Abba Kyari da barnar da ake zargin ya rika yi da tun bara aka fara tono su.”

- Pelumi Olajengbesi

A barrantar da sauran 'Yan Sanda

Olajengbesi ya na ganin akwai bukatar gaskiya tayi aikinta a lamarin Abba Kyari domin kawo karshen hada-bakin da jami’an tsaro suke yi da marasa gaskiya.

Kara karanta wannan

NDLEA sun yi kokari, abin a yaba: Kungiya ta fadi me ya kamata a yiwa Abba Kyari

Kafin yanzu, ana tuhumar Kyari da alaka da fitattun ‘yan damfara wanda yanzu suke hannu. Don haka Lauyan ya ce bai kamata gwamnati ta ba shi wani uzuri ba.

FBI ta fito ta na zargin Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi da biyan Kyari kudi har kusan N8m domin ya kama wani abokin aikinsa a hakar damfara.

Kawo yanzu, Legit.ng Hausa ba ta samu labarin cewa Sufetan ‘Yan Sanda na kasa ya yi magana a kan sabon zargin da ake yi wa wannan jami’in da aka dakatar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel