Karon farko sun hau jirgi: Martani yayin da budurwa ta share wa iyayenta hawaye
- Wata ‘yar Najeriya mai suna Mary Ogundimu ta yada hotunan iyayenta a filin jirgin sama, inda ta ce wannan ne karonsu na farko da suka hau jirgi
- Matar ta tuna da yadda iyayenta duka suka sadaukar da rayuwarsu ga ’ya’ya duk da kasancewar mahaifinta makanike da mahaifiyarta kuma ’yar kasuwa
- Mutane da yawa da suka karanta labarinta a kafar LinkedIn sun sami shauki, inda da dama suka ce suna fatan yin irin wannan karimci ga iyayensu
Wata budurwa mai suna Mary Ogundimu ta shiga shafin LinkedIn domin bayyana yadda ta sakawa iyayenta farin ciki a fuskokinsu domin saka musu da irin sadaukarwa da suka mata a rayuwa.
Ta ce a karon farko cikin tsawon shekarun da suka yi a rayuwarsu, sun sami jin damar shiga jirgin sama, lamarin da ya faranta musu.
Meye labarin wannan budurwa?
Mary ta ce ba ta damu da cewa mutane da yawa za su yi mamaki cewa ta yi wani babban al’amari na daukar nauyin tafiya ta jirgin sama ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Budurwar ta bayyana cewa mahaifinta makanike ne, mahaifiyarta kuma ‘yar kasuwa ce.
Lokacin da ta girma, ta tuna sau da yawa da za ta 'tashi' cikin gaggawa a kan acaba a jihar Legas don kawai ta halarci jarrabawar daukar aiki, wanda ta ce sau da dama takan rasa.
Allah ya ba ta uban kirki
Mary ta ba da labarin lokacin da mahaifinta zai kwana da yunwa don kawai ya tabbatar da cewa 'ya'yansa sun sami wadataccen abinci.
Ta yi addu’a ga duk wanda yake son ya yi wa iyayensa wani abin alheri amma bai da abin yi, ta ce Allah ya ba da hanyar saka wa iyaye.
Ga kadan daga cikin martanin jama'a
Vivian A. Anegbe ya ce:
"Na yi hawaye da jin wannan musamman, lokacin da kika zo batun mahaifinki na gode da wannan rubutu, madam. ♀️ Wannan ya zaburar da addu'ar sirri a cikin zuciyata cewa Allah ya albarkace na zama albarka ga iyalina."
Ehi Iden ya ce:
“Mary Ogundimu, wannan ba shine irin labarin da nake nema ba ne a kan LinkedIn da tsakar rana amma abin da Allah ya so na gani kenan domin ya san idan na karanta wannan zan sami lokacin yin tunani a kan inda ni ma na fito."
Raymond I. Emmanuel ya ce:
"Ka kaunaci gaskiyar cewa kina alfaharin gaya wa duniya wacece ke, abu ne da zai faranta miki rai. Barka da shiga sabon matakin rayuwa. Ina taya ki murna 'yar uwa."
Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata daga haduwa da su a hanyar kauye
A wani labarin, a safiyar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya hango wasu kananan yara da su ke yawo a kan titi.
Wadannan yara mata biyu suna aiki ne a sa’ilin da ya kamata a ce su na makaranta kamar yadda sauran sa’o’insu suke cikin aji a daidai wannan lokacin.
Mai magana da yawun bakin Mai girma gwamnan, Gboyega Akosile ya fitar da jawabi na musamman, ya ce gwamnati ta dauki dawainiyar yaran.
Asali: Legit.ng