'Karin Bayani: Jirgin Ƙasa Ya Yi Tsayawar Dole a Daji Saboda Ɓarnar Da Ƴan Daba Suka Yi a Hanya

'Karin Bayani: Jirgin Ƙasa Ya Yi Tsayawar Dole a Daji Saboda Ɓarnar Da Ƴan Daba Suka Yi a Hanya

  • Wasu batagari sun lalata titin jirgin kasar Legas zuwa Ibadan wanda hakan yasa sai da jirgin kasa ya tsaya cak a ranar Asabar
  • Fasinjoji da dama sun firgice inda suka tsaya wurin Papalanto bayan baro tashar jirgin kasan Obafemi Awolowo a Ibadan tun karfe 8:30 na safe
  • Da yake suna tafe da jami’an tsaro wadanda suke rike da makamai da kuma masu gyara wadanda nan da nan suka gyara titin aka ci gaba da tafiyar

Barnar da yan daba suka yi a layin dogo ya tilastawa jirgin kasa da ke zuwa Legas - Ibadan ya tsaya na dan wani lokaci a ranar Asabar, The Punch ta ruwaito.

Fasinjojin da suka shiga jirgin misalin karfe 8.30 na safen Asabar a tashr Obafemi Awolowo sun yi tsayawar dole kafin karasawa Funmilayo Ransome Kuti, a Papalanto, saboda lalata wani sashi na layin dogon.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Da Duminsa: Jirgin Kasa Ya Tsaya a Daji Ba Shiri Domin Lalata Layin Dogo Da ’Yan Daba Suka Yi
Jirgin kasa ya yi tsayawar dole a daji saboda barnar da 'yan daba suka yi. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Wani fasinja, wanda malami na a Jami'ar Ibadan, Dr Feyi Leo ya shaida wa wakilin The Punch cewa tsoro ya kama shi da sauran fasinjojin, lokacin da jirgin ya yi tsayawar ba shiri.

Nan da nan masu gyara suka gyara titin

A cewar Leo, wani jirgi da ke tafe daga Legas zuwa Ibadan ya tsaya dayan bangaren, daga nan jiragen kasan suka ci gaba da tafiya bayan an gyara titin.

Kamar yadda ta bayyana:

“Muna tafe a tsanake har muka bar tashar jirgin kasar Abeokuta, muna kusa isa Papalanto, sai jirgin ya tsaya ya koma baya.
“Nan da nan muka tsorata muka fara tambaya. Cikin gaggawa jami’an NRC suka bayar da sanarwa cewa masu gyara suna aiki kuma ba za a dade ba."

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Ba wannan bane karon farko da aka taba samun irin wannan matsalar ba

Dayan fasinjan wanda ya ce sunan sa Promise, ya ce yadda jirgin kasar ya tsaya kowa ya firgita. Amma abinda ya kwantar wa kowa da hankali shi ne yadda jami’an tsaro da masu gyaran suka yi saurin kammala gyaran.

An samu rahoto akan yadda makamancin hakan ya taba faruwa har sau biyu a watan Janairu, wanda ya ja jiragen kasan suka tsaya na mintuna 35 kafin a ci gaba da tafiyar.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164