Karin bayani: PDP ta dage taron gangamin ta a shiyyar Arewa maso Yamma
- Rahotonni sun ce, jam'iyyar PDP ta dage zaman taron gangaminta a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan
- Har zuwa yanzu dai ba a san musabbabin dage taron ba, wanda aka shirya yi a ranar 12 ga watan Fabrairu
- Jam'iyyar ta PDP ta sanar da masu ruwa da tsaki da hukumar INEC kan wannan dage taro da aka yi yau Juma'a
FCT, Abuja - Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa a ranar Juma’a ya dage taron gangamin na shiyyar Arewa maso Yamma wanda aka shirya yi a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022, Punch ta ruwaito.
Daily Post ta tattaro cewa, labarin ya fito ne daga wata sanarwa da Sakataren jam'iyyar na kasa Umar Bature ya sanyawa hannu a ranar Juma’a mai taken ‘Postponement of Northwest zone Congress’.
Bature ya ce
“Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa na son sanar da dage taron mu na gangami na shiyyar Arewa maso Yamma wanda aka shirya yi a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022.
“Za a sanar da sabon kwanan wata a kan lokaci.
"INEC, masu neman takara, wakilai da masu ruwa da tsaki duk su lura da haka, don Allah."
Duk da cewa jam’iyyar ba ta bayyana dalilan dage taron ba ba zato ba tsammani, ana iya alakanta dagewar da zaben 2022 na majalisar tarayya da za a yi a rana guda.
Buhari: Na ji dadin yadda masu hannu da shuni suka gane cewa canja Najeriya ba aikin mutum daya bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng