Alheri danko: Wata kungiyar musulunci ta kawo alheri Kaduna, ta yi aikin jinyar ido kyauta
- Wata kungiyar Muslunci ta zo da alheri, inda ta fara taimakawa marasa galihu a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Kungiyar ta ware wasu mutane da ke bukatar maganin ido, inda ta kuduri daukar nauyin yi musu magani kyauta
- Kungiyar ta bayyana adadin mutanen da suka halarta, sannan ta yi kira ga masu hannu da shuni su kawo dauki
Kaduna - Daily Trust ta rahoto cewa, wata kungiyar addinin musulunci mai suna Leen Charity Organisation ta zo da alheri, inda ta yi wa marasa galihu 100 maganin ido kyauta a jihar Kaduna.
Wanda ya kafa kungiyar ta Leen, Abdul’aziz Umar Abubakar, ya ce kungiyar tana kula da mutane ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya ce kungiyar ta fahimci cewa mafi yawan masu fama da matsalar ido ba sa iya samun magani, lura da cewa masu fama da matsalar ido kamar hakiya ana tura su cibiyar kula da ido ta kasa.
Abubakar ya ce:
“Muna da burin ganin mun faranta wa wannan rukunin na mutane saboda da yawa ba sa iya daukar nauyin maganin ido. Leen ta sami taimako kuma mun yanke shawarar taimaka wa mutane 100 da dan abinda muke da su."
Abubakar ya bayyana cewa kusan mutane 500 ne suka zo neman taimako amma 100 ne kawai za a iya dubawa, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa kungiyar saboda Allah domin a tallafawa karin mutane.
Ya kara da cewa kungiyar ta taimaka wa mutane da dama a Kaduna, Abuja da Adamawa musamman marayu a lokacin bukukuwan Sallah.
Wani ya gina makarantar firamare a kungurmin kauye
Yayin da mutane da dama ke koka yadda gwamnati ta gaza wajen tabbatar da ingantaccen ilimi ga alummar kasar nan, wani mutum a jihar Gombe ya zo da sabon tsarin habaka ilimi.
Ambasada Habu Ibrahim Gwani, wani mazaunin jihar Gombe ne da ya gina wata makarantar firamare a wani kungurmin kauye mai suna Agangaro da ba kowace irin mota ce ke iya shiga ba.
Kauyen Agangaro, wanda hedkwata ne ga wasu rugagen Fulani a yankin Gwani yamma ta karamar hukumar Yamaltu a jihar Gombe, a zagaye yake da mutane da dama, wadanda ke rayuwa ba tare da sanin yadda ake karatu da rubutu ba.
Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe, ya yi tattaki wajen taron budewa da mika makarantar ga gwamnatin jiha har wurin da aka yi ginin, inda ya tattaro bayanai tare da tattaunawa da mutumin da ya yi wannan aikin.
Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata daga haduwa da su a hanyar kauye
A wani labarin, a safiyar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya hango wasu kananan yara da su ke yawo a kan titi.
Wadannan yara mata biyu suna aiki ne a sa’ilin da ya kamata a ce su na makaranta kamar yadda sauran sa’o’insu suke cikin aji a daidai wannan lokacin.
Mai magana da yawun bakin Mai girma gwamnan, Gboyega Akosile ya fitar da jawabi na musamman, ya ce gwamnati ta dauki dawainiyar yaran.
Asali: Legit.ng