Karfin hali: Aisha Buhari ta cire tsoro, ta hau jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja

Karfin hali: Aisha Buhari ta cire tsoro, ta hau jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja

  • Uwargidan shugaban kasa ta cire tsoro ta yi tafiya a jirgin kasa daga jihar Kaduna zuwa Abuja ranar Alhamis
  • Wannan na zuwa ne yayin da ta kai wata ziyara a jihar Kano, inda ta gana da gwamnan jihar kan wasu batutuwa
  • Majiyoyi sun shaida cewa, Aisha Buhari ta bi hanyar Abuja zuwa Kaduna da jirgin kasan ne domin karfafa gwiwar 'yan Najeriya

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a ranar Alhamis ta hau jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, matakin da mai taimaka mata ta ce ta yi shi ne domin karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da su yi amfani da hanyar.

Premium Times ta rahoto cewa ta samu labarin Aisha Buhari ta iso Kaduna ne daga Kano ta jirgin sama sannan ta yanke shawarar tafiya ta jirgin kasa zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya jihar Kano, ta yi jawabi mai ratsa zuciya

Aisha Buhari a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja
Karfin hali: Duk da rashin tsaro, Aisha Buhari ta hau jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ta kasance tare da kaninta Mahmud Ahmad wanda aka fi sani da Modi da wasu mataimakanta.

Wadanda suka san tafiyar tata sun ce jirgin kasan ya bar Kaduna da misalin karfe 4 na yamma ya isa Abuja da misalin karfe 6 na yamma a ranar.

Majiyar ta ce Aisha Buhari da 'yan uwanta suna tafiya ta jirgin sama ne tun lokacin da mijinta ya hau kan karagar mulki a 2015. A ko da yaushe dangin na tafiya ne da jiragen saman fadar shugaban kasar da aka tanadar na musamman.

Wannan shi ne karon farko da ta yi doguwar tafiya ta a jirgin kasa, kamar yadda daya daga cikin hadimanta ta shaida wa majiya.

Hanyar Abuja-Kaduna na fuskantar barazana

Biyo bayan sace-sacen mutane da ake yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, yawancin matafiya a Najeriya sun yi watsi da bin hanyar inda suka fara tafiya tsakanin garuruwan biyu ta jirgin kasa.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kashe kudade masu tarin yawa wajen inganta harkar sufurin jiragen kasa a Najeriya.

Baya ga hanyar Abuja zuwa Kaduna, layin dogo daga Legas zuwa Ibadan ma ya tashi ya fara aiki gadan-gadan.

Hakazalika, gwamnatin Najeriya na ci gaba da bayyana bukatar nemo kudade domin cigaba da aikin layin dogo a Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Hanifa Abubakar: Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace wajibi a yi adalci

A wani labarin, uwar gidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta kai ziyara jihar Kano domin jajantawa gwamnati da al'umma bisa kisan Hanifa Abubakar da rasuwar fitaccen Malami, Dakta Ahmad Bamba.

A wani taron manema labarai da ta yi a gidan gwamnati, Aisha tace ta kawo ziyara ne a kashin kanta domin ta yi ta'aziyya ga iyalan mutanen biyu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

Aisha ta ce:

"Na zo nan jihar ne a karan kaina domin jajantawa gwamnan jihar Kano da matarsa, Sarkin Kano da kuma sauran mazauna jihar bisa rashin fitaccen malami, Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.