Da dumi-dumi: Majalisa ta umarci NNPC ta dakatar da wadanda suka shigo da gurbataccen fetur
- Gwamnatin Najeriya karkashin NNPC ta gano wasu kamfanonin da suka shigo da gurbataccen man fetur kasar nan
- Wannan lamari ya jawo cece-kuce a Najeriya, wannan yasa majalisar wakilai ta ce dole a dauki mataki a kai
- Majalisar ta ba da umarnin gaggawa ga kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC kan dakatar da kamfanonin hudu
FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da ya dakatar da kamfanonin da ke da hannu wajen shigo da man fetur da aka gurbata da sinadarin methanol.
Majalisar ta kuma bukaci hukumar NNPC din da ta mika sunayen kamfanonin ga kwamitin ta domin gudanar da cikakken bincike, inji rahoton TheCable.
An zartas da hakan ne yayin zaman majalissar da aka yi a ranar Alhamis 10 ga watan Fabarairu bayan amincewa da kudirin da Mohammed Monguno ya dauki nauyinta.
Mele Kyari, Manajan Darakta na Kamfanin NNPC Limited, ya ce MRS, Oando, Emadeb Consortium, da Duke Oil, wani reshen NNPC ne suka shigo da man da aka gurbata da methanol a wannan karon, kamar yadda Channels Tv ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk lafinin NNPC ne
Da yake ba da gudunmuwa kan kudirin, Onofiok Luke, dan majalisa daga jihar Akwa Ibom, ya ce duk laifin kamfanin NNPC yasa aka shigo da gurbataccen man fetur daga kasashen waje.
Luke ya bukaci majalisar da ta dauki mataki kan lamarin don tabbatar da dawo da kwarin gwiwar ‘yan Najeriya.
Toby Okechukwu, mataimakin shugaban marasa rinjaye, ya ce kamfanin NNPC bai yi aikin da ya dace ba a matsayinsa na hukumar gudanarwa. Ya ce majalisar ta gudanar da bincike da dama kan badakalar da hukumar NNPC ta yi.
Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai
A wani rahotonmu na baya kunji cewa, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.
Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.
A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.
Asali: Legit.ng