Zargin ta'addanci: Wani jirgin sama na ta yawo a Bauchi, gwamna ya matsu, NAF ta fara bincike
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna damuwarsa kan tsaron al’ummar jiharsa saboda wasu dalilai
- Gwamnan ya sanar da rundunar sojojin saman Najeriya game da yawon wani jirgin sama mai saukar ungulu da ake zargin ko da yaushe ana gani a dajin Bauchi
- Rundunar sojin sama ta kuma baiwa gwamnan tabbacin gudanar da cikakken bincike kan bayanai da kuma kasancewar jirgin mai saukar ungulu a jihar
Jihar Bauchi - Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike don gano tushen wani jirgin sama mai saukar ungulu da ake zargin yana shawagi a dajin Lame-Burra a kananan hukumomin Toro da Ningi na jihar Bauchi.
Leadership ta ruwaito cewa binciken da rundunar sojin saman ta fara gudanarwa ya fara ne bayan da gwamnan jihar, Bala Mohammed ya bayar da rahoto game da jirgin da har yanzu ba a tantance na su waye ba.
Da yake jan hankalin rundunar sojin sama kan wannan lamari mai ban al’ajabi a lokacin ziyarar ban girma da sabon hafsan sojin sama na musamman na NAF a Bauchi, Air Vice Marshal Tajudeen Yusuf, Gwamna Mohammed ya ce lamarin ya haifar da damuwa ga jihar.
Ya bayyana cewa dajin ya kai kimanin hekta 205,900 kuma ya yi iyaka da jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton sirri game da jirgin
Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, gwamnan ya bayyana cewa, rahotannin tsaro na sirri sun nuna cewa jirgin mai saukar ungulu na shawagi a cikin dajin.
Ya ce kasancewar jirgin da ake zargin shawaginsa a jihar ya sanya damuwa game da lafiyar mutanen da ke zaune a yankin.
Mohammed ya ce:
"Mu ba masu kin mutane masu zuwa bane ko baki, kawai dai ba ma maraba da masu aikata laifuka a cikin jiharmu."
Jami’in rundunar sojin saman Najeriya ya mayar da martani
A martaninsa kan rahoton gwamnan, Yusuf ya ce NAF na sane da lamarin kuma tuni ta fara gudanar da bincike a kan haka.
Ya yabawa gwamnan bisa yadda yake kula da tsaron jama’arsa da jihar baki daya tare da yin kira ga jama’a da su taimaka wa NAF da duk wasu bayanan da suka dace domin gudanar da bincike.
A wani labarin, wata kotun jihar Legas dake Ikeja ranar Laraba ta garkame jami'an hukumar Sibil Defens -Amarachukwu Asonta da Adebayo Ajayi, 32 kan zargin laifin fashi da makami.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa Mai Shari'a Oyindamola Ogala ta bada umurnin garkamesu ne bayan sun musanta zargin da ake musu.
Hukumar DPP ta gwamnatin jihar Legas ce ta shigar da su kotu.
Asali: Legit.ng