Rashin tsaro: Tuni na rubuta wasiyya ta, iyalina ba za su yi rikici kan gado ba, Gwamna Ortom
- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa shi dai tuni ya rubuta wasiyyarsa kuma ko yanzu ya mutu ya sha miya tunda ya wuce shekaru sittin
- Kamar yadda Ortom ya sanar da ma'aikatan ASCON da suka ziyarcesa, ya ce iyalansa ba za su yi rikici kan kadarorin da ya bar musu na gado ba
- Ortom ya koka da yadda tsaron kasar nan ya lalace da yadda ya ki shiru kan lamarin, wanda hakan yasa wasu ke farautar rayuwarsa
Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa tuni shi ya rubuta wasiyyarsa sakamakon hauhawar rashin tsaron da ya addabi kasar Najeriya.
Kamar yadda aka san gwamnan da batun rashin tsaron kasar nan, gwamnan ya ce ya na da tabbacin cewa iyalansa ba za su yi fada kan gadon da ya bar musu ba idan wani abu ya faru da shi.
Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karba wakilan Administrative Staff College of Nigeria (ASCON) wadanda suka samu shugabancin darakta janara, Mrs Cecilia Gayya a gidan gwamnatin jihar da ke garin Makurdi.
Me gwamnan yace kan matsalar tsaro?
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamnan ya ce:
"Tuni na rubuta wasiyyata. Ba na tsoron kowa. Idan na mutu yanzu, na san iyalina ba za su fada a kan abinda na bar musu na gado ba. Na riga na fadi abinda nake so.
"Da kuma jama'ar da ke shiru a kan abinda ke faruwa a kasar Najeriya, ina son sanar da su cewa suna da 'ya'ya. Tabbas, shiru kamar yarda ce. Don haka, dole ne 'yan Najeriya su jajirce kan shaidancin da ke faruwa."
A ruwayar jaridar Vanguard, gwamnan ya ce:
Ya cigaba da cewa: "Ni na yi bangare na kuma na dauka alkawarin cewa babu wanda ya isa ya tsorata ni. Na wuce shekaru sittin, Ubangiji ya ba ni. Ubangiji ya yi min baiwa kuma na gode masa."
"Toh don haka kada wanda ya yi tunanin cewa zai iya kange Samuel Ortom a wannan rayuwar. Amma na yarda cewa Ubnagiji zai bani kariya kamar yadda ya saba bani. An dinga kokarin ganin a kawar da ni, a kashe ni amma Ubangiji ya dinga ba ni kariya," gwamnan yace.
Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kiran ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.
A wata takarda wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur ya saki, ya yanko inda gwamnan ya ce kungiyar tana kawo tashin hankali a Binuwai.
Asali: Legit.ng