Mutum hudu sun mutu yayin da yan bindiga suka kone kauye baki ɗaya a Kaduna
- Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai kazamin hari yankin karamar hukumar Zangon Kataf dake kudancin jihar Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun kashe mutum huɗu, sannan kuma suka ƙona ƙauyen Sabon Kaura baki ɗaya
- A cewar wani mazaunin yankin mutane da dama sun jikkata yayin da wasu suka ɓata ba'a san inda suka shiga ba
Kaduna - Mutum huɗu aka tabbatar sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka ƙone kauyen Sabon Ƙaura dake yankin Aytap, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya shaida wa jaridar The Nation cewa zai tuntuɓi kwamandan dake kula da Zangon Kataf, kafin ya sanar a hukumance.
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa maharan sun farmaki ƙauyen ne ranar Talata da daddare, suka aikata wannan ɗanyen aikin.
Mayaƙan Fulani ne suka kai harin
Sai dai wani mazaunin yankin, wanda ya yi zargin cewa yan bindigan mayaƙan Fulani ne, ya ce:
"Abin da muka gano yanzu kusan kowane gida dake ƙauyen yan bindiga sun kona shi. Muna zargin mayaƙan Fulani ne suka zo ɗaruruwan su domin kaddamar da shirin su."
"Mutum huɗu muka tabbata sun rasa rayukan su yayin da mutane da dama suka ɓata ba'a san inda suka yi ba. Ba zan iya tabbatar da adadin mutanen da suka jikkata ba a harin."
"Baki ɗaya yan ƙauyen sun shiga babban tashin hankali, jami'an tsaro biyar ne kacal a garin lokacin da yan ta'addan suka shigo yankin, kuma ba za su iya fafata wa da su ba."
A kwanakin nan dai yan bindiga sun ƙara yawaita kai hare-hare yankunan jihar Kaduna, musamman kudancin jihar.
A wani labarin na daban kuma Yan bindigan cikin kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa a Ogun
Yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun bindige wani hamshakin ɗan kasuwa a Gidan man fetur na jahar Ogun.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun zo a cikin kayan sojiji, suka harbe mutumin a kai, sannan suka yi gaba da wasu kuɗaɗe dake cikin motarsa.
Asali: Legit.ng